Search
Subscribe
Majalisa ta baiwa kwamiti umarnin tantance Emefiele

Gwamnan Babban Bakin Najeriya, Godwin Emefiele

Majalisa ta baiwa kwamiti umarnin tantance Emefiele

A yau Talata majalisar dattawa ta baiwa kwamitin da ke bada rahotonnin bankuna, inshora da cibiyoyin kudade, da su tantance Gwamnan Babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a cikin mako guda kuma su mika rahoton su ga zauren majalisar dattawan.

A makon jiya ne Shugaba Buhari ya sake nada Emefiele a karo na biyu inda zai yi wa’adin shekara biyar a matsayin Gwamnan CBN.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin