Search
Subscribe
Majalisa ta ce a cire sunan Al-Makura daga gine-ginen gwamnatin Nasarawa

Majalisa ta ce a cire sunan Al-Makura daga gine-ginen gwamnatin Nasarawa

Gwamna Umaru Tanko Al-makura na Jihar NasarawaMajalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta umarci Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya cire sunayensa a gine-gine da kaddarorin gwamnatin jihar ko su dauki makaki a kansa.
Majalisar ta bayar da umurnin ne a Lafiya lokacin da ta gayyaci wasu jami’an gwamnatin jihar uku da suka hada da Mai ba Gwamnan Shawara a kan Harkokin Jam’iyyu Hajiya Hajarat Ibrahim danyaro da Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Injiniya Wada Muhammed da kuma shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta Jihar (SUBEB) Alhaji Abdulkareem Abdullahi don amsa tamboyoyin da suka shafi jihar.
 ’Yan majalisar sun fara ne da tambayar Shugaban Hukumar SUBEB Alhaji Abdulkareem Abdullahi iya bayyana dalilin da ya sa aka lakaba wa ginin makarantar zamani ta gwamnati da Gwamna Al-Makura ya gina a kwanakin baya a Bukan-Sidi da ke Lafifya sunan Ta’al Model Nursery, Primary and Junior Secondary School, kuma aka shafa mata launi irin na Jam’iyyar CPC.
Shugaban wanda ya ce majalisar tana da damar gudanar da irin wannan bincike, ya ce amma duk tsare-tsare da ayyukan gine-ginen sun samu amincewar Hukumar Ilimi Bai-daya ta kasa (NUBEC) sai dai launin ne kawai ya zamanto ayar tambaya.
Shi ma a nasa bangaren da yake amsa tambayar majalisar game da babura masu tayu uku (Keke NAPEP) da Gwamna Al-Makura ya sayo kwanakin baya da aka lakaba musu suna Keke Taa’al wato takaitaccen sunan Gwamnan, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri Injiniya Wada Muhammed ya ce an yi amfani da wannan suna ne domin tunawa da irin gagarumin ci gaba da Gwamnan ya kawo a bangaren sufuri a cikin garin Lafiya da kewaye bayan ya kammala wa’adinsa na mulki.
Ya ce gwamnatin jihar ta sayo baburan 200 ne a kan Naira miliyan 93 sabodahaka a cewarsa aka ga ya dace a yaba wa Gwamnan shi ya sa aka lakaba musu sunan Keke Taa’al.
A bangaren mai ba Gwamna shawara ,Hajiya Hajarat Ibrahim danyaro kuma, Shugaban Majalisar Alhaji Musa Ahmed Muhammed ya ce majalisar ta yanke shawarar umarta Gwamna Al-Makura ne ya sallame ta, don a cewarsa ta nuna wa ’yan majalisar rashin da’a a zauren majalisar a lokacin da suka gayyace ta, don ta amsa wasu tamboyoyi a kan wani zargi da suke yi mata na cewa ta bayyana a wata jarida cewa gwamnatin jihar ta ba ’yan majalisar Naira miliyan 300 su raba a matsayin kudin hutu da haka ya jefa ’yan majalisar cikin rudani. Ya ce wannan magana karya ta yi, saboda haka ba ta girmama ’yan majalisar ba.
 Ya kara da cewa bayan an tattauna batun, majalisar ta bukace ta da ta ba ’yan majalisar hakuri amma ta ki. Hakan a cewarsa ya sa suka ba da umarni a cire ta.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin