Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Majalisa ta dage zama don juyayin rasuwar Sanata Osinowo

Zauren Majalisar Dattawa ta Najeriya

Majalisa ta dage zama don juyayin rasuwar Sanata Osinowo

Majalisar Dattawa ta Najeriya ta dage zamanta zuwa ranar Laraba 1 ga watan Yuli domin zaman makokin Sanata Adebayo Sikiru Osinowo da ya rasu a lokacin hutunta.

Zaman Majalisar na ranar Talata ya yi shiru na minti daya domin jimamin rasuwar dan majalisar mai wakiltar Legas ta Gabasa, wanda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, yana dan shekara 64.

Dage zaman bisa al’adar majalisar kamar yadda Sanata Yahaya Abdullahi, Shugaban Masu Rinjay ya bukata, ya samu goyon bayan Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Ovie Omo-Agege, da ya jagoranci zaman na ranar Talata, ya sanar da dage zaman bayan yabon mamcin da kuma yi masa addu’a.

Sanatocin da suka rasu daga 2019

Sanata Osinowo shi ne dan Majalisar hudu ta ya rasa ransa a majalisar a shekara daya na Majalisar ta tara.

Sauran ukun su ne Benjamin Uwajumogu daga jihar Imo, Ignatius Logjan daga jihar Filato, da kuam Rose Okoji  daga jihar Kuros Riba.

Baya ga su, wasu Mutum 15 sun rasu a Majalisar tun daga 1999 da Najeriya ta sake dawowa mulkin demokuradiyya.

 

‘Yan Majalisar Walai da suka rasu daga 2019

Bayan sanatocin da suka rasu, ‘yan wakilai da suka rasu daga 2019 da aka rantsar da majisar su ne Jafaru Iliyasu Auna daga Jihar Neja da kuma Muhammad Adamu Fagen-Gawo daga jihar Jigawa.