✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta hana TCN kirkiro ayyukan lantarki a 2021

Majalisar Wakilai ta dakatar da Hukumar Samar da Wutar Lantarki kirkirar sabbin ayyuka.

Majalisar Wakilai ta dakatar da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (TCN) kirkirar sabbin ayyuka a 2021.

Majalisar ta ce maimakon kirkiro sabbin ayyukan samar da wutar lantarki a ba, gara TCN ta kammala wadanda ta riga ta faro.

Shugaban Kwamitin Majalisar kan Wutar Lantarki, Magaji Da’u Aliyu ya yi bayanin ne lokacin da shugabannin TCN ke bayanin kasafin hukumar na badi da yadda suka aiwatar da na 2020.

Bayanin nasa na zuwa ne bayan Manajan Daraktan TCN, Sule Abdulaziz, ya shaida wa kwamitin cewa hukumar na da manyan ayyuka 158 da ta fara aiwatarwa tun daga shekarar 2011.

Manajan Daraktan ya ce hukumar na shirin fara wasu sabbin ayyuka guda 14 a 2021 kuma an sanya su a cikin kasafi.

Ya ce nisan da ayyuka guda 119 da hukumar ke aiwatarwa na tsakanin kashi 0 zuwa 95% da kammaluwa.

Ayyukan a cewarsa sun hada da na layukan wutar lantarki 45, kananan tashoshin lantarki 70, da ayyuka hudu na kara karfin kayan lantarki.

Ya ce an a halin yanzu an kammala gina kananan tashoshin lantarki 28 da layukan lantarki guda 11.

Akwai kuma ayyuka 25 da aka kammala aka kaddamarwa kuma an gama biyan ‘yan kwangilan; sai wasu 14 kuma hukumar ta kaddamar bayan an kammala su, amma ba ta gama biyan ‘yan kwangila ba.

Sai dai kwamitin Majalisa bai yi na’am da sabbin ayyukan ba, inda ya ce ce gara an kammala wadanda aka riga aka faro tun daga baya.