✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa za ta binciki zargin cin zarafin da Sanata Elisha ya yi

A yau Laraba Majalisar dattawa za ta fara binciken badakalar cin zarafin wata da ake zargin Sanata Elisha Cliff ya yi a wani Shago a…

A yau Laraba Majalisar dattawa za ta fara binciken badakalar cin zarafin wata da ake zargin Sanata Elisha Cliff ya yi a wani Shago a Abuja.

An dai ta yada bidiyon yadda Sanatan ya ci zarafin wata a shagon a shafukan sada zumunta na zamani a ranar Talata.

Sanata Uba Sani, da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya ne ya yi kira ga majalisar Dattawa da ta binciki Sanatan.

Abin  ya faru ne a ranar 11 Ga Mayu, kafin a rantsar da su, a Abuja.

Sanata Uba Sani, ya ce ya amsa kiran waya sama da mutum 111 daga yammacin jiya Talata zuwa safiyar yau Laraba daga cikin Najeriya zuwa kasashen waje wanda ya ce hakan babban cin mutunci ne ga mai mukamin Sanata a Najeriya.