✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Aljeriya ta soke shirin gudanar da zaben Shugaban Kasa

Majalisar Tsarin Mulkin Kasar Aljeriya ta soke gudanar da zaben Shugaban Kasa da aka shirya yinsa a ranar 4 ga watan, bisa matsalolin da ta…

Majalisar Tsarin Mulkin Kasar Aljeriya ta soke gudanar da zaben Shugaban Kasa da aka shirya yinsa a ranar 4 ga watan, bisa matsalolin da ta kira na rashin ’yan takara da tsawaita lokacin mayar da mulkin siyasa da kuma barazanar fushi daga masu zanga-zanga.

Akwai yiwuwar wannan matakin ya tsaiwaita mulkin rikon kwarya na shugaba Abdelkader Bensalah, wanda aka tsara zai ci gaba da zama shugaban kasa har sai an zabi sabon Shugaban Kasar.

An kawo karshen mulkin shekaru 20 na Shugaba Abdelaziz Bouteflika watanni biyu da suka gabata, sakamakon matsin lamba daga masu zanga-zangar ya sauka daga mulki.

Sai dai an ci gaba da gudanar da jerin zanga-zangar neman shugaban rikon kwaryar da ya sauka, da nufin kawo karshen kane-kanen da ’yan boko suka yi a madafun ikon kasar wanda suke damawa tun samun yancin kan kasar daga Faransa a shekarar 1962.

Wani mai sharhi akan siyasar kasar, Farid Ferrahi, ya ce akwai yiyuwar shugaba Bensalah ya share fiye da kwanaki 90 akan gadon mulki, idan dai har ba a iya gudanar da zaben ba, lamarin da zai kara fusata masu zanga-zangar.

Cikin wani jawabi ta kafar Telebijin, majalisar tsarin mulkin kasar, wadda ita ce ke kula da mayar da mulki ga zabebben shugaba, ta ce ’yan biyu ne kacal suka nuna sha’awarsu ta shiga takarar, sai dai ana ganin ba su cancanta ba.

Wata majiyar siyasar kasar ta fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa wadannan ’yan takara biyu da suka nuna sha’awarsu, wadanda kuma ba sanannu ne a idon ’yan kasar ba-sun gagara samun saka hannun akalla mutune dubu 600.

Sai dai ita majalisar ba ta sanya sabuwar ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasar ba. Amma ta bukaci shugaba Bensalahn da ya shirya zaben a wata rana ta daban. An dai nada Bensalah a matsayin shugaba na rikon kwarya har zuwa ranar 9 ga watan Yulin bana.