Da Dumi Dumi

Majalisar Amurka na ci gaba da binciken tsige Trump

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Majalisar Dokokin Amurka ta saurari shaidu da yawa a binciken yuwuwar tsige shugaban Amurka Donald Trump a bainar jama’a.

WASHINGTON DC –

An fara sauraren ne da safiyar Talata tare da shaidu uku da kuma abin da suka sani akan zargin da ake yiwa Shugaba Trump na yunkurin tursasawa Ukraine ta binciki abokan hamayyarsa.

Duka dai, kwamitocin Majalsir Wakilan sun saurari shaidu tara ne a lokacin zama biyar daban daban da aka yi ranakun Talata da Laraba da kuma Alhamis na wannan makon.

Sai dai shaidar da aka fi saka ido ta zone daga jakadan Amurka a kasashen Tarayyar Turai da ya bada gudummuwar dala miliyan daya ga kwamitin shirye shiryen rantsar da shugaba Trump, Gordon Sondland.

ADVERTISEMENT

Da alama Sondland ya taka rawar gani a tattaunawar tare da Ukraine akan zargin da ake yi cewa Shugaba Trump ya bukaci Ukraine ta binciki wanda ake ganin zai kalubalance shi a zaben Shugaban kasa na 2020, kuma tsohon mataimakin Shugaban Amurka, Joe Biden, akan cin hanci.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya