Da Dumi Dumi

Majalisar Amurka ta fara tunanin tsige Trump daga mulki

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban wani kwamiti mai karfin iko a Majalisar Dokokin Amurka ya ce kalaman da Shugaban Kasar Donald Trump ya yi a tattaunar da ya yi ta tarho da Shugaban Ukraine na iya bayar da damar a tsige shi daga mukaminsa.

Adam Schiff wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sa Ido Kan Bayanan Sirri da Tsaron Amurka, yana matsa wa Fadar White House ta saki cikakkun bayanan tattaunawar.

Mista Schiff, ya ce idan ta tabbata Mista Trump na kokarin tursasa wa Shugaban wata kasa ya ba shi bayanan sirri kan wani abokin hamayyarsa a siyasa, to babu makawa sakamakon laifin da ya aikata zai kasance a iya tsige shi daga kan mukaminsa.

Rahotanni daga Amurka na cewa Shugaba Donald Trump ya matsa wa Shugaban Ukraine Bolodmir Zelenski ya sake gudanar da bincike kan dan Joe Biden, wanda shi ke kan gaba wajen neman zama dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar Democrat.

Dan Mista Biden din mai suna Hunter Biden ya taba yin aiki a wani kamfanin samar da makamashi a kasar Ukraine lokacin mahaifinsa na rike da mukamin Mataimakin Shugaban Kasa zamanin Barack Obama.

ADVERTISEMENT

Mista Trump ya amince cewa ya tattauna kan batun kuma ya ambaci sunan Joe Biden a yayin tattaunawarsu, kuma ya ce yana da ’yancin yin haka.

Mista Biden ya ce Mista Trump ya aikata babban laifi-kuma ya bukaci a gudanar da bincike kan batun.

Kawo yanzu dai Fadar White House ba ta ce komai ba kan lamarin.

Share