✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta amince da Ministocin Buhari 43

Bayan kammala tantance sunayen sababbin Ministocin da Shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa, majalisar ta amince da kuma tabbatar da sunayen Ministoci 43 Shugaba…

Bayan kammala tantance sunayen sababbin Ministocin da Shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa, majalisar ta amince da kuma tabbatar da sunayen Ministoci 43

Shugaba Buhari ya aikawa Majalisar ne dan neman sahalewarsu akan sunayen, a matsayin wadanda za a nada mukaman ministoci. Sahalewar a yau, ta biyo bayan kwanaki biyar da majalisar ta dauka tana tantance ministocin. 22 cikin su, sun kawai rusunawa zauren majalisar ne; sa’annan suka fice, kamar dai yadda majalisar ta bukace su da su yi.

Shugaban majalisar, Ahmed Lawan, ya ambaci sunayen Ministocin, inda yake tambayar zauren ko sun amince da a nada su mukaman Ministocin, amma dukkan ‘yan Majalisar Dattawan sun ce, sun yi na’am da a nada su, mukaman Ministocin Najeriya.

Ministocin da aka tantance sun hada da: Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Sanata Rotimi Amaechi (Rivers), Uchechukwu Ogah (Abia) Sanata George Akume (Benue), Ogbonnaya Onu (Ebonyi), Emeka Nwajuaba (Imo), Sanata Adeleke Mamora (Lagos), Olamilekan Adegbite (Ogun), Adamu Adamu (Bauchi), Sharon Ikeazor (Anambra) da Mustapha Baba Shehuri (Borno)

Sauran su ne: Timipre Sylva (Bayelsa), Sanata Chris Ngige (Anambra), Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti), Manjo Janar  (Mai ritaya) Bashir Salihi Magashi (Kano), Ramatu Tijani (Kogi), Mohammed Abdullahi (Nasarawa), Tayo Alasoadura (Ondo), Abubakar D. Aliyu (Yobe) Zubairu Dada (Niger), Sunday Dare (Oyo) da Mohammed Musa Bello (Adamawa).

Sai kuma: Sadiya Umar Farouk (Zamfara), Zainab Ahmed (Kaduna), Osagie Ehanire (Edo),Sen Hadi Sirika (Katsina), Abubakar Malami (Kebbi), Paulen Tallen (Plateau), Muhammadu Maigari Dingyadi (Sakkwato), Festus Keyamo (Delta), Ali Isa Pantami (Gombe), Gbemisola Saraki (Kwara) da Goddy Jedy-Agba (Cross River). Da kuma Sulaiman Adamu (Jigawa), Maryam Katagun (Bauchi), Clement Agba (Edo), Geoffrey Onyeama (Enugu), Muhammad Mahmoud (Kaduna) Babatunde Raji Fashola (Lagos), Rauf Aregbesola (Osun), Sabo Nanono (Kano), Lai Mohammed (Kwara) da Saleh Mamman (Taraba).