✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta amince da sabon kasafin kudi

Majalisar Dattawa ta amince da kasafin kudin 2020 na Naira tiriliyan 10.801 da aka yi wa gyaran fuska. Majalisar ta kara biliyan N292 a kan…

Majalisar Dattawa ta amince da kasafin kudin 2020 na Naira tiriliyan 10.801 da aka yi wa gyaran fuska.

Majalisar ta kara biliyan N292 a kan sabon kasafin tiriliyan N10.509 da Shugaba Buhari ya yi wa gyaran fuska.

A watan Disamban 2019 Majalisar ta amince da kasafin 2020 na Naira tiriliyan 10.594 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.

Daga baya Gwamantin Tarayya ta rage yawan kasafin saboda karyewar farashin mai a duniya da kuma raguwar kudaden shigan da kasar ta yi hasashen samu a 2020, sakamakon annobar COVID-19.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da amincewarsu da sabon kasafin bayan karbar rahoto daga Shugaban Kwamintin Kasafi na Majalisar, Sanata Barau Jibrin.

Sabon kasafin ya ware biliyan N422.775 ga hukumomi da ma’aikatun gwamnati, da kuma tiriliyan N2.952 domin biyan basuka.
Tiriliyan N4.938 kuma za a yi amfani da su ne a ayyukan yau da kullum sai kuma tiriliyan N2.488 da aka ware wa ayyukan raya kasa.

Ahmed Lawan ya bukacin kwamitocin Majalisar da su yi tsaye a aikinsu na sa ido kan yadda ake aiwatar da ayyukan da aka ware wa kudade a kasafin.

Tun da farko a ranar Laraba Majalisar Wakilai ta amince da sabon kasafin da bangaren zartarwa ya gabatar.