Da Dumi Dumi

Majalisar Dattawa ta nada manyan jami’anta

Ahmed Lawan
Ahmed Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya bayyana sunayen manyan jam’ian da za su jagorancin ayyukan majalisar, inda Sanata Abdullahi Abubakar Yahaya daga Jihar Kebbi ya zama Shugaban Masu Rinjaye, sai Ajayi Borofice daga Jihar Ondo ya Mataimakinsa, sai tsohon Gwamnan Jihar Abiya Orji Uzor Kalu ya zama  Babban Mai tsawatarwa, shi kuwa Sanata Abdullahi Aliyu Sabi daga Jihar Neja ya zama Mataimakinsa.

Mukamin Shugaban Marasa Rinjaye ya tafi ga Enyinnaya Abaribe  daga Jihar Abiya, sai Sanata Emmanuel Bwacha daga Jihar Taraba, Mataimakinsa. Shi kuwa Sanata Philip Tanimu Aduda daga Birnin Tarayya ne ya zama Mai tsawatarwa Bangaren Marasa Rinjaye, Sanata Sahabi Ya’u, Mataimakinsa.

Sanarwar ta biyo bayan takardun bukatar haka daga shugabannin jam’iyyun APC  da PDP, Adams Oshiomhole da Yarima Uche Secondus.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya