Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Majalisar Dattawa ta Nada Shugabannin Kwamitoci

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana sunayen shugabannin kwamitocin majalisar.

Wadanda aka nada din sun hada da Sanata Jibrin Barau da zai jagoranci Kwamitin kasafin kudi, inda Adeola Olamilekan zai shugabanci kwamitin Kudi, Dauda Jika kuwa zai kula da Kwamitin ‘Yan sanda, Aliyu Magatakarda shi zai shugabanci Kwamitin Tsaro, Sanata Ali Ndume aka nada a matsayin shugaban kwamitin Sojoji, Abdullahi Adamu aikin gona, Bala Ibn Na’Allah kula da kwamitin sojan sama, sai Suleiman Kwari shi zai shugabanci kwamitin dakile cin hanci da rashawa,Dino Malaye harkar sufurin jiragen sama, Sanata Uba Sani zai shugabanci kwamitin harkokin inshorar bankuna da sauran cibiyoyin kudade, Oluremi Tinubu zata shugabanci kwamitin harkar sadarwa.

ADVERTISEMENT

An kuma nada Peter Nwabaoshi shugaban kwamitin raya yankin Neja-Delta, Adamu Abdullahi kwamitin ayyukan noma sannan Sanata Kabiru Gaya zai shugabanci kwamitin hukumar zabe, sauran sun hada da Rochas Okorocha ala’adu da yawan bude ido, Danjuma Goje kwamitin yada labarai da ala’amuran jama’a, inda Sanata Kashim Shettima zai jagoranci kwamitin harkokin cikin gida, Ibrahim Geidam shi ne zai shugabanci kwamitin kwadago, Sanata Malam Ibrahim Shekarau kuma ya na shugabantar kwamitin kula da harkokin ma’aikatun gwamnati da dai sauransu.

ADVERTISEMENT