Da Dumi Dumi

Majalisar Dinkin Duniya ta shawarci Najeriya ta sa haraji kan kangayen gidaje

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari

Wata jami’ar Majalisar Dinkin Duniya, mai suna Leilani Fartha, ta yi kira ga Najeriya ta fito da tsarin biyan haraji ga kangayen gidajen da babu kowa a cikinsu.

Leilani Fartha, wadda ita ce jami’ar rajin ’yancin samar da wadatattun gidaje, ta ce idan Najeriya ta fito da wannan haraji, za ta rage matsalar karancin muhalli da take fuskanta. Kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa a shafinta na Intanet.

Ta bada wannan shawara ce a wani taron ’yan jarida a Abuja, inda ta nuna damuwa game da halin zaman kuncin da ’yan Najeriya ke rayuwa ciki a wasu yankunan ‘share-wuri-zauna’ da ke gefen Abuja.

Leilani ta ce kashi 69 cikin 100 na al’ummar kasar nan suna zaune ne a irin wadannan matsugunai wadanda da dama daga cikinsu ba su da ababen bukatun rayuwa, kamar ruwan sha da wuraren kula da lafiya.

“Sannan kuma babu tsaro, a kullum suna tunanin za a iya korarsu daga inda suke zaune.Kwana 10 da muka yi muna bincike da nazari a Najeriya, mun gano irin zaman kashin-dankalin da ake yi a kasar nan. Hakan ya fi karfi ne wajen nuna fifiko ko bambancin muhalli da wurin zama.

ADVERTISEMENT

“Akwai matsalar karancin gidaje har miliyan 22 da akalla ake bukata cikin gaggawa. A lokaci guda kuma sai manya-manya gine-gine ake ta yi a cikin birane, wadanda wasu ma kafin a yi ginin sai an tashi masu karamin karfi, an raba su da inda suke,” inji ta.

Ta ce “Irin wadannan gine-gine ba su cike gurabun bukatar muhalli. Da yawansu ma haka suke kasancewa babu kowa a cikinsu na tsawon shekaru da dama. Sun zama hanyar almundahana da karkatar da kudaden jama’a.”

Kuma ta yi kira ga gwamnati ta gaggauta shawo kan matsalar muhalli da kuncin talauci, sannan ta nemi a kafa dokar daina korar masu kananan karfi daga gidajensu musamman a birnin Abuja.

Share