✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan Gabas ta Tsakiya

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce Gabas ta Tsakiya ba za ta iya daukar wani sabon rikici ba a yanzu.…

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce Gabas ta Tsakiya ba za ta iya daukar wani sabon rikici ba a yanzu.

A yayin taron manema labarai da aka saba gabatarwa a kowace rana, Dujarric ya ce daga ranar Juma’a zuwa yau suna ganin hare-hare da makamai masu linzami, na roka da na jiragen sama a kasashen Isra’ila da Zirin Gaza da Lebanon da Siriya da Iraki da Saudiyya. Kamar yadda Sakatare Janar Antonio Guterres yake fada a koyaushe Gabas ta Tsakiya ba za ta iya daukar sabon rikici ba.

A ranar 25 ga Agusta jiragen yaki marasa matuka na Isra’ila sun fado a Beirut babban birnin Lebanon.

A farkon watan nan a yankin Beka na gabashin kasar an kai harin bam ta sama sau uku da daddare kan sansanin Kungiyar Falasdinawa ta FHKC/GK.

Jiragen saman yaki marasa matuka da na ruwa na yaki da na sama na yaki na Isra’ila na karya ka’idar amfani da iyakokin Lebanon. ’Yan kasar kuma na mika wannan matsala ga Majalisar Dinkin Duniya.

’Yan tawayen Houthi na Yemen da Iran ke taimakawa kuma sun sanar da kai hari da jiragen sama marasa matuka kan sansanin sojoji a Riyadh babban birnin Saudiyya. Sai dai Saudiyyar ba ta fitar da wata sanarwa ba game da wannan batu.