✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Birtaniya ta yi watsi da kiran a gudanar da sabon zabe

A karo na biyu, Majalisar Dokokin Birtaniya ta yi watsi da shirin Firayi Minista Boris Johnson na gudanar da zabe da wuri, a wani yunkuri na…

A karo na biyu, Majalisar Dokokin Birtaniya ta yi watsi da shirin Firayi Minista Boris Johnson na gudanar da zabe da wuri, a wani yunkuri na ganin ba a saba wa wa’adin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai (EU) ba.

Johnson ya so a goyi bayan niyyarsa ta gudanar da zaben gaggawa ranar 15 ga Oktoba, a yunkurinsa na neman samun rinjaye a majalisar, saboda ta amince da tsarinsa na shirin ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai, gabanin babban taron shugabannin kungiyar ta EU.

Bayan kuri’ar bijirewa da aka kada a ranar Litinin da ta gabata, Johnson ya aiwatar da shirin nan nasa da ake takaddama a kai, na dakatar da Majalisar Dokokin na tsawon mako biyar, har sai Sarauniyar Ingila ta gabatar da jawabinta na shekara- shekara ga majalisar, mai kunshe da bayanin shirin ayyukan majalisar da gwamnati za ta aiwatar a shekara mai zuwa.

Watsi da gudanar da wani sabon zabe da majalisar ta yi, na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan da Sarauniya Elizabeth ta Ingila, ta bayyana goyon bayanta ga kudirin dokar hana Johnson aiwatar da shirinsa na ficewa daga Tarayyar Turai a ranar 31 ga Oktoba, ba tare da an zayyana yarjajeniyar rabuwar ba.