✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da ’ya’yanta biyu

Wutar rikici ta fara ruruwa a Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, bayan da majalisar ta bada sanarwar dakatar da wadansu ’yan majalisar biyu na tsawon wata,…

Wutar rikici ta fara ruruwa a Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, bayan da majalisar ta bada sanarwar dakatar da wadansu ’yan majalisar biyu na tsawon wata, Wadanda aka dakatar su ne Sani Isiya Gumel da ke wakiltar Mazabar Gumel da Malam Aminu Sule Sankara da ke wakiltar Ringim. An dakatar da su ne saboda majalisar ta samu damar gudanar da bincike a kan wasu laifuffuka da ake zargin sun aikata.

Shugaban Kwamitin Watsa Labarai na Majalisar Malam Aminu Zakari Gwiwa ne ya bayyana dakatarwar, inda ya ce ana zarginsu sne da laifin kokarin zare wasu takardu a Ma’aikatar Kudi kan wata almundahana da ’yan majalisar suka tafka a ma’aikatar daga shekarar 2015 zuwa 2017. Ya ce wannan ya sa majalisar ta kafa kwamitin bincike a kansu.

Da yake mayar da martani Malam Sani Isiya Gumel ya ce lokacin yin maganarsu shi da abokinsa Aminu Sule Sankara bai yi ba, saboda bai san laifin da suka yi ba.

Wannan yunkuri na dakatar da ’yan majalisar ya haifar da ka-ce-na-ce a tsakanin magoya bayan ’yan majalisar biyu da aka dakatar da kuma wadanda suke goyan bayan Shugaban Majalisar.

Sai dai wadansu na kallon al’amarin da cewa bita-da-kulli ne ake yi wa ’yan majalisar da suke tare da tsohon Shugaban Majalisar Malam Isa Idris Gwaram.