Da Dumi Dumi

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta koma zama a makarantar firamare

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta koma da zama a wata sabuwar makarantar firamare da aka gina a garin Gusau, fadar gwamnatin jihar, kuma  hakan ya biyo bayan aikin sabunta ginin majalisar da ake kan yi ne a yanzu haka.

Malam Mustafa Jafaru-Kaura, wanda shi ne Jami’in Hulda da Jama’a na Majalisar ya sanar da haka a cikin wata sanarwa a Gusau.

Gwamnan Jihar Alhaji Bello Matawalle ne a kwanakin baya ya bayar da kwangilar aikin sabunta ginin majalisar. “Lura da aikin sabunta ginin majalisar jihar da gwamnatin jihar ta bayar, a yanzu majalisar ta kaura zuwa wani wajen da ba na dindindin ba.

“Wannan wajen kuma ya kasance sabon ginin wata makarantar firamare ce da aka kammala bada jimawa ba, wacce ke daura da Hedkwatar Hukumar Kula da Ilimin Bai-Daya ta Jihar da ke a Gusau,” kamar yadda Jafaru-Kaura ya fadi a cikin sanarwar.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya