✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Gombe ta tsige Mataimakin Shugabanta

A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan Majalisar Dokokin Jihar Gombe 21 daga cikin 24 suka tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Shu’aibu Adamu Haruna daga…

A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan Majalisar Dokokin Jihar Gombe 21 daga cikin 24 suka tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Shu’aibu Adamu Haruna daga Mazabar Kwami ta Gabas, inda suka maye gurbinsa da Siddi Buba, daga Kwami ta Yamma.

Alhaji Adamu Saleh Pata, dan majalisa mai wakiltar Yamaltu ta Gabas ce ya gabatar da bukatar tsige Mataimakin Shugaban Majalisar inda ya karanto sunayen ’yan majalisa 21 cikin 24 da suka goyi bayan tsige Alhaji Shu’iabu Adamu, inda dan majalisa daga Billiri ta Gabas kuma Shugaban Kwamitin Watsa Labarai na Majalisar Mista Tulfugut Meme Kardi, ya goyi bayan bukatar.

Dan majalisa mai wakiltar Akko ta Gabas Alhaji Mohammed Abubakar Luggerawal ne ya ba da sunan Siddi Buba daga Kwami ta Yamma don maye gurbin Shu’aibu Adamu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.

Musthapha Usman Hassan, dan Majalisar Gombe ta Kudu ya goya masa baya, inda nan take majalisar ta amince ba hamayya.

Da Shugaban Majalisar Abubakar Sadik Ibrahim Kurba ya tambayi majalisar ko sun amince  ko akwai wanda yake da wani zabi sai suka ce sun amince.

Akawun Majalisar Barista Rukayya Jalo, ta ce idan irin haka ya faru kundin tsarin mulkin 1999 sashi na 94 da aka yi wa gyara ya ba da dama majalisa nan take ta rantsar da sabon Mataimakin Shugaban Majalisar don ya kama aiki kuma hakan aka yi.

Da yake zantawa da manema labarai Shugaban Kwamitin Labarai, Tulfugut Meme Kardi, ya ce a yanzu ba za su bayyana dalilan  tsige tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ba sai nan gaba.

’Yan majalisar sun tafka muhawara a kan wasu kudirori da Gwamnatin Jihar Gombe ta tura gaban majalisar. Kudirorin biyu su ne kudirin kafa Hukumar Asusun Kiwon Lafiya na Jihar da na Hukumar Kula da Asibitocin Jihar. Kuma bayan tafka muhawara sai Shugaban Majalisar ya mika kudirorin ga kwamitocin kiwon lafiya da na kudi domin tattara rahoto a kansu.

Majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga wannan wata.