✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar jihar Legas taki amincewa da mutum 3 cikin wanda za a tantance su

Majalisar jihar Legas tayi watsi da mutum uku cikin 38 da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya aike wa majalisar. Mutum uku da ‘yan majalisun suka…

Majalisar jihar Legas tayi watsi da mutum uku cikin 38 da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya aike wa majalisar.

Mutum uku da ‘yan majalisun suka ki amincewa dasu sun hadar da: Ajaiye Obembe da Prince Lanre Sanusi sai Obafemi George.

Zauren majalisar dokokin Jihar Legas

Da misalin karfe 12 na ranar yau zuwa yammaci majalisar ta Legas tayi aikin tantance mutanen da Gwamnan ya aike mata domin ta tantance su a matsayin Kwamishinonin da za su yi aiki a sabuwar gwamnatinsa, aikin tantancewar da kakakin majalisar Honurabul Mudassiru Obasa, ya jagoranta a zauren majalisar.