Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Majalisar Kano ta dakatar da Shugaban KASCO

Mjalisar Dokokin Jihar Kano ta bayar da sanarwar dakatar da Manajan Darakta na Kamfanin Taki na Jihar Kano (KASCO), Alhaji Bala Muhammad Inuwa saboda gazawa ya bayyana gaban majlaisar don kare kasafin kuxin kamfanin na bana.

Da yake bayar da sanarwar, Shugaban Kwamitin Harkokin Kasafin Kuxi na Majalisar, Alhaji Tasi’u Rabi’u Fanisau ya ce majalisar ta xauki wannan mataki ne a kan Shugaban KASCO akamakon qin zuwa a karo na biyu da ya yi don kare kasafin kuxin kamfaninsa wanda ke qarqashin Ma’aikatar Ayyukan Gona ta Jihar Kano.

ADVERTISEMENT

“Da farko ya zo majalisar, sai dai kasancewar bai zo da abin da ake buqata ba kwamitin ya umarce shi ya je ya gyara kasafin kuxinsa ya dawo da shi daga baya. Sai dai tun daga wancan lokaci bai dawo ba, kuma an yi ta kiransa ya zo ya kawo gyaran da aka ba shi na kasafin kuxin amma ya qi zuwa har kwamitin ya gama zamansa. Don haka kwamiti ya zartar da cewa babu wani abu da aka fitar na kasafin kuxi wanda ya shafi kamfanin na KASCO, ma’ana an sa musu abin da ake cewa 0-allocation,” inji Fanisau.

Tuni Kwamitin Kasafin Kuxi na Majalisar ya aike wa Gwamnatin Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da umarnin dakatar da Shugaban KASCO xin tare da naxa wani sabon shugaban riqon kamfanin.

ADVERTISEMENT