✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Kano ta dakatar da wakilanta 5

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da wakilanta biyar sakamakon rigimar da ta barke a majalisar a makon jiya. Da yake sanar da dakatarwar ga…

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da wakilanta biyar sakamakon rigimar da ta barke a majalisar a makon jiya.

Da yake sanar da dakatarwar ga ’yan majalisar bayan dawo da zama da majalisar ta yi a ranar Litinin Shugaban Majalisar, Alhaji  Abdul’aziz Garba Gafasa ya ce an dakatar da ’yan majalisar ne saboda rashin da’a da karya dokokin majalisar.

’Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Alhaji Garba Ya’u Gwarmai wakilin mazabar Kunchi da Tsanyawa da Alhaji Labaran Abdul Madari mai wakiltar Warawa da Alhaji Isiyaku Alhaji Ali Danja wakilin Gezawa da kuma Alhaji Mohammed Bello wakilin mazabar Rimin Gado da Tofa. Sai kuma Alhaji Salisu Ahmed Gwangwazo wakilin Birni da Kewaye.

A cewar Shugaban Majalisar “An dakatar da ’yan majalisar biyar saboda karya dokokin majalisar inda suka hargitsa zaman majalisar tare da hana ci gaba da gudanar da ayyukan majalisar wanda hakan ya saba da dokar majalisar ta IB karamin sashi na 4 (a) da  (b) da (d) da (e). Haka kuma sun yi kokarin dauke sandar majalisar wanda hakan yake nuni da niyyarsu ta yi wa zaman majalisar karan-tsaye.”

Idan za a tuna a ranar Litinin din makon jiya ne yayin zaman majalisar wadansu ’yan majalisar suka yi kokarin hana zaman majalisar saboda sun fahimci kwamitin majalisar da aka dora wa alhakin bincikar tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II zai mika rahotonsa, inda zai bayar da shawarar tube Sarkin, lamarin da ya janyo aka ba hammata iska har aka dage zaman majalisar zuwa Litinin ta wannan mako.