Da Dumi Dumi

Majalisar Kano ta kafa kwamitin da zai binciki Sarkin Kano bisa ‘yi wa al’adu karan-tsaye’

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi
Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi

Majalisar Dokokin Jihar Kano a karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Abdul’aziz Garba Gafasa ta umarci kwamitinta da ke kula da korafe- korafen jama’a ya binciki zargin da ake yi wa Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II kan wasu halaye da yake yi da suka ci karo da al’adu da mutuncin al’ummar Jihar.

Majalisar ta bayar da wannan umarnin ne bayan kudirin da Shugaban Kwamitin Kananan Hukumomi a Majalisar Alhaji Zubairu Hamza Masu ya gabatar.

Dan majalisa Zubairu Hamza Masu ya shaida wa majalisar cewa kwamitinsa ya karbi korafin ne daga wata kungiya da ke fafutikar ci gaban ilimi da al’adu  a karkashin shugabancin Muhammad Bello Abdullahi da kuma Muhammad Mukhtar Jaen inda suka zargi Sarkin cewa yana nuna halayen da suke zubar da kimar al’ummar Jihar Kano,

Bayan da aka tatatauna majalisar ta  mika korafin ga kwamitinta na korafe-korafe  inda aka ba kwamitin wa’adin mako guda ya mika rahoton bincikensa.

Har ila yau majalisar  ta dauki Mataimakin Shugaban Majalisar Hamisu Ibrahim Chidari da Shugaban Masu Rinjaye, Kabiru Hassan Dashi da Mai tsawatarwa na majalisar Tasi’u Ibrahim su hadu da mambobin wancan kwamitin  don gudanar da aikin binciken Sarkin da aka dora musu.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya