Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Majalisar kolin shari’ar Musulunci ta nemi a kafa ’yan sintiri a kauyuka 

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III

Majalisar kolin shari’ar Musulunci ta nemi a kafa ’yan sintiri a kauyuka 

Majalisa Koli ta tabbatar da Shari’ar Musulunci rashen jihar Kaduna ta yi kira ga jama’a mazauna kauyuka da‎ su kafa ‘yan sintiri domin kare rayukansu da dukiyoyinsu daga mahara.

Majalisar ta fitar da wannan sako ne a cikin kasidar da ta fitar bayan taron gaggawa da ta gudanar a jihar Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Shaikh Abdulkareem Hashim Bindawa, wanda ya karanta sakon ya ce, hakika Majalisar ta damu da rashin tsaro da ke faruwa a kananan Hukumomin: Zariya, Chikun, Igabi, Zariya da Birnin-Gwari.