Majalisa Koli ta tabbatar da Shari’ar Musulunci rashen jihar Kaduna ta yi kira ga jama’a mazauna kauyuka da su kafa ‘yan sintiri domin kare rayukansu da dukiyoyinsu daga mahara.
Majalisar ta fitar da wannan sako ne a cikin kasidar da ta fitar bayan taron gaggawa da ta gudanar a jihar Kaduna.
Mataimakin Shugaban Majalisar Shaikh Abdulkareem Hashim Bindawa, wanda ya karanta sakon ya ce, hakika Majalisar ta damu da rashin tsaro da ke faruwa a kananan Hukumomin: Zariya, Chikun, Igabi, Zariya da Birnin-Gwari.