✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Wakilai na shirin daidaita rikicin Majalisar Jihar Bauchi

Majalisar Wakilai ta fara yunkurin shiga tsakani game da rikicin shugabanci da ya turnuke a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi. Majalisar ta tura wakilanta zuwa jihar…

Majalisar Wakilai ta fara yunkurin shiga tsakani game da rikicin shugabanci da ya turnuke a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi.

Majalisar ta tura wakilanta zuwa jihar don bin bahasi da kuma sasanta bangarori biyu na majalisar

Da yake tarbar wakilan majalisar, Gwamnan Jihar Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ya ce gwamnatin jihar na matukar jin kunyar wannan matsala da ta dabaibaye majalisar kusan wata guda.

Ya ce koda yake ita siyasa lamarinta haka ya gada ana samun sabanin fahimta wadansu su zo da riginmgimu wadansu na alheri wadansu kuwa sabanin haka, ya ce a shirye yake ya yi biyayya ga al’ummar jihar. Ya ce, yana girmama ’yancin cin gashin kai na Majalisar Wakilai, amma abin da ya faru a Bauchi abin jimami ne.

Gwamna Bala ya ce gwamnatinsa ba za ta tsoma baki wajen aikin da kwamitin zai yi ba illa dai zai ba su duk goyon bayan da suke bukata don su samu nasarar ayyukan da za su yi. “Mu dai a iya saninmu Majalisar Dokoki daya ce a Jihar Bauchi, kuma an yi zabe inda aka zabi shugabannin majalisa kamar yadda doka ta ce,  kuma na sanya hannu kan takardar izinin bude majalisa kuma an yi zabe tare da Akawun Majalisa da sandar iko na majalisa,’ inji shi.

Ya ce abin kunya ne a ce ga gwamnatin da tsofaffin sanatoci ke jagoranta su yi  wani abu da zai kaskantar da majalisa, wadda ita ce murhu na biyu na mulkin dimokuradiyya. Kuma ita ce sitiyarin tafiyar da gwamnati da ba za su taba yin katsalanda ba a cikin gudanar da ayyukanta.

Gwamnan ya ce a matsayinsa na Gwamnan da ya samu goyon bayan al’umma ba zai taba yin wani abu da zai kawo rashin girmama wani dan majalisa ba, ya kuma bai wa kwamitin tabbacin cewa gwamnati za ta amince da dukkan shawarwarin da za su bayar kuma ya yi fatar cewa dukkan bangarorin biyu za su amince da abin da kwamitin ya hukunta gare su.

Shugaban Kwamitin Alhaji Musa Sarkin Adar ya ce Shugaban Majalisar Wakilai ne ya nada su don su binciki halin da majalisar ke ciki inda aka ce an samu mutum biyu da suke ikirarin shugabancin majalisar. Ya ce rufe majalisar da aka yi ya tsayar da dukkan ayyukan majalisar wanda haka ba daidai ba ne.

Sai ya roki hadin kan gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi don kwamitin ya ji dadin gudanar da ayyukansa.

Kwamitin ya saurari bahasin lamarin daga bakin masu ruwa-da-tsaki a jihar.

Kuma al’ummar jihar sun zuba ido su ga ko wakilan kwamiti za su iya warware matsalar.