✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Wakilai ta bukaci manyan hafsoshi su sauka

Majalisar Wakilai ta bukaci manyan hafsoshin sojin Najeriya su yi murabus saboda gazawa wajen kawo karshen matsalar tsaro. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin…

Majalisar Wakilai ta bukaci manyan hafsoshin sojin Najeriya su yi murabus saboda gazawa wajen kawo karshen matsalar tsaro.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta-baci a kan harkar tsaro.

A zaman Majalisar Wakilai a shekaranjiya Laraba, ta yi kira ga Shugaba Buhari ya sallami manyan hafoshin sojin idan suka ki sauka da kansu.

Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Mohammed Mongunu (APC daga Borno) ne ya gabatar da wannan bukata a yayin zaman majalisar.

Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci zaman, inda majalisar ta amince da bukatar Mongunu na, “A magance matsalar ci gaba da hare-hare da ake yi a yankin Arewa ta Gabas.”

Da yake karin bayani, dan majalisa Ahmadu Jaha na Jam’iyyar APC daga Jihar Borno cewa ya yi ya kamata Shugaba Buhari ya sallami shugabannin sojin.

Mongunu ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da samun hare-haren Boko Haram. “Kwanan nan, ’yan ta’adda sun tursasa wa sojoji rufe hanyar Damaturu zuwa Maiduguri. Kuma ita ce kadai hanyar fitowa daga Maiduguri zuwa sauran sassan kasar nan. Rufe hanyar na nuna cewa Boko Haram sun kwace hanyar ke nan,” inji shi.

Manyan hafsoshin su ne Babban Hafsan Tsaro, Janar Gabriel Abayomi Olonishakin da Babban Hafsan Sojojin Sama, Iya Mashal Sadik Abubakar da Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Bayis Admiral Ibok-Ete Ekwe, sai Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftana Janar Tukur Buratai.

Aminiya ta ruwaito cewa an ba su makaman ne a karon farko a watan Yulin shekarar 2015 domin su yi shekara 2 bayan rantsar da Shugaba Buhari. Sai aka kara musu shekara 2, wanda shi ma ya kare a Yulin bara.

Bayan batun shekarunsu da ya ja da kuma dadewa da suka yi kan mukaman, sashi na 09 da 08 na kundin tsarin harkar tsaron kasar nan (NTACOS), ya ce, “Duk hafsan da aka ba mukamin Babban Hafsa na sojan sama, ko na kasa ko ruwa ko na tsaro, zai rike mukamin ne na shekara biyu. Za a kara masa shekara biyu bayan na farko.”

Ana tunanin an bar su ne domin kasancewar rashin zaman lafiya da ake fama da shi a sassa daba-daban na kasar nan.

A nata bangaren, Majalisar Dattawa cewa ta yi Shugaba Buhari ya yi gaggawar sanya dokar ta-baci a kan tsaro.

Majalisar ta yanke wannan shawara ce bayan kusan awa 6 sanatocin suna tattaunawa a kan batun karuwar rashin tsaro a kasar nan.

Ba mu muka nada kanmu ba-Manyan Hafsoshi

Da suke mayar da martani kan batun, Kakakin Hedkwatar Tsaro, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya cehedkwatar tsaro ba ta da hakkin zabar manyan hafsoshi.

Ya kara da cewa batun zaba da cirewa ko canja manyan hafsoshin sojoji hakki ne na Shugaban Kasa.