Search
Subscribe
Majalisun Nasarawa da Gombe sun wanke  kwamishinoni, Katsina da Kwara za su fara tantance nasu

Majalisun Nasarawa da Gombe sun wanke  kwamishinoni, Katsina da Kwara za su fara tantance nasu

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta tantance tare da amincewa da sunayen kwamishinoni 15 da Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule ya mika mata. Majalisar ta tantance mutum 9 a ranar Litinin, inda ta tantance 6 a ranar Talata a zaman da ta yi karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi.

Sababbin kwamishinonin da aka tantance sun hada da Ahmed Baba Yahaya daga Karamar Hukumar Toto da Philip Dada (Karu) da Othman Bala Adam (Keffi) da Dokta Abdulkarim Abubakar Kana (Kokona) da Obadiah Boyi (Akwanga) da Yusuf Aliyu Turaki (Awe) da Salihu Ahmad Alizaga (Nasarawa-Eggon) da Farfesa Otaki Allahnana (Keana) da Misis Fati Jimeta Sabo (Nasarawa) da sauransu. Shugaban Majalisar ya bukaci sababbin kwamishinonin su gudanar da ayyukansu ba tare da jin tsoro ba ko son kai ba.

Daga Gombe majalisar ta tantance sunayen mutum 21 da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya aike mata. Shugaban Majalisar Abubakar Sadik Ibrahim ne ya bayyana sunaye sabbabin kwamishinonin. Cikin wadanda aka tantance a shekaranjiya Laraba da jiya Alhamis sun hada da Barista Zubairu Mohammed Umar (Funakaye) da Ibrahim Dasuki Jalo Waziri (Gombe) da Mohammed Magaji Gettado (Akko) da Dokta Ahmed Gana (Gombe) da Mista Julius Ishaya (Kaltungo) da Dokta Hussaina Danjuma Goje (Akko) da sauransu.

Hakazalika daga Jihar Katsina Gwamna Aminu Bello Masari ya aike da sunayen mutanen da yake bukatar a tantance domin nadawa kwamishinoni a jihar, inda majalisar ta ajiye ranar Litinin mai zuwa don fara tantance su.  Shugaban Masu Rinjaye ya karanto jerin sunayen a gaban majalisar da  suka hada da Musa Adamu Funtuwa (Funtuwa) da Ya’u Umar Gwajogwajo(Mai’aduwa) da Tasi’u Dahiru Dandagoro (Batagarawa) da Abdullahi Imam (Musawa) da sauransu.

Shi kuwa Gwamna Abdulrahaman Abdulrazak na Jihar Kwara, mika sunayen mata 9 ya yi da maza 7 ga Majalisar Dokokin Jihar domin ya samun amincewarta, don nada su kwamishinoni. Shugaban Majalisar Dokokin Alhaji Yakubu Danladi ya ce majalisar ta ajiye ranar Talata mai zuwa domin fara aikin tantance sunayen da Gwamnan ya aike musu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin