✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Asasul Islam ta fitar da sababbin tsare-tsaren koyarwa

Daraktan Makarantar Asasul Islam ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa da ke Unguwar Randar Ruwa Rikkos a Jos Jihar Filato, Ustaz…

Daraktan Makarantar Asasul Islam ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa da ke Unguwar Randar Ruwa Rikkos a Jos Jihar Filato, Ustaz Muhammad Muhammad Abubakar ya bayyana vewa bisa tsare-tsaren da suka yi wa makarantar, da yardar Allah za ta zama abin koyi ga dukan makarantun kungiyar da ke viki da wajen Najeriya.

Malamin ya bayyana haka ne a lokavin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ve a sabuwar makaranta mai  ajujuwa 12 da ofisoshin gudanarwa da wani bawan Allah, Alhaji Abubakar Sulaiman ya gina, kuma ya bai wa kungiyar ta kasa, suna son su gudanar da makarantar kananan yara da firamare da sakandare.

Har ila yau ya ve suna son da yamma su rika karantar da tarbyiyar Musulunvi a makarantar da sanin makamar harshen Larabvi da haddar Alkur’ani Mai girma da muhimman abubuwan addinin Musulunvi.

Ya ve za su rika gabatar da karatu a ranakun Asabar da Lahadi don matan aure da magidanta, wadanda ba su riga sun yi karatun addinin Musulunvi ba. Ya ve mutum ko ya yi karatun boko, ya je har jami’a ya yi digiri, akwai bukatar ya zo ya yi karatun addini. Don haka a ranakun na Asabar da Lahadi za su rika karantar da matan aure da safe kuma su karantar magidanta da yamma.

“Abin da ya karfafa mana gwiwar kawo wadannan sababbin tsare-tsare a wannan makaranta shi ne, dama muna da irin wadannan makarantu na Asasul Islam a dukan fadin Najeriya. Don haka ne muke son mu mai da wannan makaranta ta musamman da za mu inganta harkokin koyarwa ta hanyar samar da kayayyakin aiki na zamani da koyar da ilimin kwanfuta da ilimin kimiyya da samo kwararrun malamai don ganin daliban makarantar sun samu ingantatven ilimi. Domin mu nuna wa sauran makarantunmu a aikave-aikaven da suka kamata su yi,” inji shi.

Shugaban ya ve suna son su yi tafiya daidai da zamani, ta yadda daliban da suka samu shiga makarantar, za su rika fita da abubuwan da suka kamata don wuvewa makarantun gaba, kamar jami’o’i da sauran manyan makarantu ba tare da wata matsala ba.

Ya yi kira ga al’umma su ba su goyon baya da hadin kai, domin su samu nasarar vimma kudurori da suka sanya a gaba.