✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Little Angel ta yaye dalibai 28 a Katsina 

An yi kira ga iyaye da su kara mayar da hankali a wajen harkokin karatun ’ya’yansu domin ganin cewa, sun zama masu amfani a tsakanin…

An yi kira ga iyaye da su kara mayar da hankali a wajen harkokin karatun ’ya’yansu domin ganin cewa, sun zama masu amfani a tsakanin al’umma. Wadda ta assasa makarantar Uwargida Hajiya Hadiza Musa Danladi ce ta baiyana haka a wajen bikin yaye daliban makarantar a zangon karatu na shekarar 2018/2019 da aka yi a harabar makaranta da ke unguwar GRA a cikin garin Katsina.

“Mun yi kokarin kammala kawo kayan aiki a dakin karatu na makarantar tare da wajen koyon aiki da na’ura mai kwakwalwa Kwamfuta wajen cin abinci da sauran su domin karawa daliban kwarin gwiwa. Sannan muna kara ba malamai dama da kayan aiki domin kara sanin hanyoyin koyo da koyarwa”, in ji ta.

Makarantar wadda ke da sassan kananan yara, firamare, karamar sakandire da babba, wadda kuma aka rufe zangon karatunta a wannan lokacin tare da yawan dalibai 680, daga cikin su aka yaye daliban babbar Sakandire 28 bayan samun nasarar cin jarabawar WAEC da NECO. Daga cikin abubuwan da suka kayatar a wajen wannan biki sun hada da muhawarar akan ‘Tsakanin Malamai da Iyaye ko wa yafi bayar da gudunmuwa a wajen ci gaban yara? Sai kuma raye-rayen gargajiya. Daga karshe, Shugaban Makarantar Mai Shari’a Musa Danladi, kuma Babban Jojin Jahar, ya yaba da irin gudunmuwar da makarantar take samu daga iyaye da kuma gwamnati gami da daidaikun wasu mutane.