Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Makarantar Ma’ahad Ashabil Kahfi ta yaye dalibai

Makarantar Islamiyya ta Ma’ahad Ashabil Kahfi da ke Rigasa a Karamar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna ta yaye dalibai goma sha hudu. Ta yi bikin yaye daliban ne a harabar makarantar a ranar Lahadin da ta gabata.

Da yake jawabi ga Aminiya Shugaban Makarantar Malam Jamilu Ibrahim Inuwa ya ce saukar shi ne karo na biyar tun bayan kafa makarantar kimanin shekaru biyar da suka wuce.

ADVERTISEMENT

Ya ce sun fara karatu a makarantar ne da dalibai 50, amma a yanzu haka makarantar na da dalibai 400. Malamin ya kuma bayyana wasu daga cikin matsalolin da makarantar ke fama da su wanda ya ce sun hada da rashin fili na din-din da za a ce mallakinsu ne.

“Baya ga wannan akwai matsalar rashin biyan kudin makaranta akan lokaci da wasu iyaye ba su yi. Dan haka sai ya yi roko ga iyaye da su tashi tsaye wajen mayar da hankali kan ilmantar da ’ya’yansu,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Sannan a karshe ya kuma mika godiyarsa ga wadanda suka samu halartar saukar karatun, musamman wasu daga cikin iyayen daliban, kana ya kuma ja hankalin daliban maza biyar mata tara da suka sauke Alkur’ani Mai Girma da su ci gaba da lazimtarsa sau da kafa.