✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Ma’ahad Zumratul-Rahamayat ta yi bikin sauka

A makon da ya gabata ne aka yi bikin yaye daliban makarantar Ma’ahad Zumratul-Rahamayat da ke cikin garin Benin, bayan sun kammala karatun Alkur’ani mai…

Daliban makarantar Ma’ahad Zumratul-rahamayatA makon da ya gabata ne aka yi bikin yaye daliban makarantar Ma’ahad Zumratul-Rahamayat da ke cikin garin Benin, bayan sun kammala karatun Alkur’ani mai girma.
Taron bikin, wanda ya samu halartar manyan maluma na addinin Musulunci na yankunan kasar Yarabawa da kuma na sauran yankuna, ya tara ’yan kasuwa da wasu shugabannin al’umma da ke garin Benin Jihar Edo.  
Babban bako kuma shugaban limamai na kabilar Yarabawa mazauna birnin Benin, Alfa Abdulrazaki ya yi wa jama’a nasihohin jawo hankali da kira da shawara domin gyaran halayya a kan ayyukan ibada da mu’amala tsakanin juna ta yadda za a dore da zaman.
Sannan an yi irin wannan bikin a harabar makarantar Khalid Bin Walid da ke Eyaen, tare da daurin auren diyar Alhaji Sharif Ibrahim Arab Shuwa, mai suna Maryam, wadda ta sauke Alkur’ani da wani malamin addini kuma dan kasuwa mai suna Fakih Harun.
A taron bikin ne Ustaz Abubaka Yashe, babban limamin kungiyar Izala ya yi wa al’ummar musulmi bayani kan muhimmancin aure  da darajarsa, inda ya kawo misalai da dama cikin Alkur’ani da hadisan Manzon Allah. Yayin da Alaramma Malam Rabi’u na darikar Tijjaniya ya yi nasiha kan muhimmancin ilimin addini, musamman na Alkur’ani, wanda ya nuna wajibi ne iyaye su fi maida hankali a kan koya wa ’ya’yansu karatunsa tare da tarbiyya ta Musulunci.