✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Markazus Sunnah ta yaye dalibai a garin Mpampe Abuja

Makarantar Markazus Sunnah Al’islamiyya da ke garin Mpmpe Abuja ta yi bikin yaye dalibai karo na biyu, bayan kafa ta a shekarar 2008. Babban Daraktan…

Makarantar Markazus Sunnah Al’islamiyya da ke garin Mpmpe Abuja ta yi bikin yaye dalibai karo na biyu, bayan kafa ta a shekarar 2008.

Babban Daraktan makarantar, Imam Aminu Abdurrahman ya bayyana wa mahalarta bikin yayen, wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata a masallacin Masjidus Sahaba da ke yankin cewa, daliban da aka yaye su ne mata 10 da maza 13.

Malamin, wanda har ila yau shi ne Babban Limamin Masallacin, ya tabo tarihin makarantar tare da gode wa Alllah a kan nasarorin da ta samu bayan kafuwarta, inda a yanzu take da wajen karatu na kanta.

A jawabin shugaban malamai na makarantar Malam Abdurrahman Ibrahim Al-Bidawi, wanda masu garkuwa da mutane suka kama shi mako uku da suka gabata a hanyar Abuja zuwa Kaduna, kamar yadda daraktan ya gabatar, ya gode wa Allah tare da mika godiya ga iyaye da sauran jama’ar garin a kan addu’o’in da suka rika yi masa a kan lamarin, wanda a sakamakon hakan aka dage bikin yaye daliban a baya zuwa wannan lokacin, bayan ya samu kansa.

Daya daga cikin iyayen daliban, Malam Umar Gombe, wanda ’yarsa Maryam ta kasance ta daya a cikin daliban da aka yaye, ya mika godiya ga hukumar makarantar a madadin iyayen. Iyayen daliban ne dai da kansu suka mika takardun shaidar kammala makaranta ga ’ya’yan nasu a yayin bikin, wanda Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Jiragen Sama na IRS, Alhaji Muhammad Bello Makama ya jagoranta.