✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Tazkiyya ta Kafanchan ta yaye mahaddatan Kur’ani

A ranar Lahadi da ta gabata ce Makarantar Tazkiyya da ke garin Kafanchan ta yi bikin saukar karatun Kur’ani Mai girma tare da wadansu dalibai…

A ranar Lahadi da ta gabata ce Makarantar Tazkiyya da ke garin Kafanchan ta yi bikin saukar karatun Kur’ani Mai girma tare da wadansu dalibai uku da suka haddace Alkur’ani Mai girma cikin shekara uku da kafa makarantar.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Makarantun Tazkiyya ta Kasa, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya jinjina wa malaman makarantar bisa namijin kokarin da suka nuna wajen koyar da daliban, inda ya ce dama sun assasa makarantun Tazkiyya ne domin samar da mahaddata Alkur’ani Mai girma da kuma tarbiyyar Musulunci don tsarkake al’umma da kasa da kuma duniya baki daya.

Farfesa Ibrahim Makari, ya kuma yaba wa Mai martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa Muhammad II bisa kokarin da yake yi wajen bayar da gudunmawa a harkokin addini a masarautarsa.

A jawabin Sarkin Jama’a kuma Shugaban Taron, Alhaji  Muhammadu Isa Muhammad II, ya mika godiyarsa ce ga Farfesa Makari bisa irin alherin da ya kawo masarautarsa, inda ya nuna farin cikinsa tare da yaba wannan kokari.

Sarkin, wanda ya yi addu’ar zaman lafiya da kuma albarka ga mahaddatan, ya yi fatan yawaitan ire-irensu a garin, inda ya yi kira gare su da su zamo masu kyawawan dabi’u ta yadda da an gan su an ga masu riko da Alkur’ani.

Tunda farko da suke jawabi, malaman makarantar da suka hada da sashin boko da na addini, sun yi kira ga iyayen yara su rika bai wa ’ya’yansu goyon baya ta hanyar wadata su da duk abin da neman ilimi ke bukata don sauke nauyin da ke kansu.

Wannan shi ne karo na farko da makarantar Tazkiyya da ke Kafanchan da aka kafa shekara uku da suka wuce ta fara saukar karatu.