✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantun Allo: Ina ma dai…

A ranar Talata 25 ga Fabrairun da ya gabata ne yayin bikin kaddamar da shirin koyar da ilimin zamani a makarantun allo na Jihar Kano…

A ranar Talata 25 ga Fabrairun da ya gabata ne yayin bikin kaddamar da shirin koyar da ilimin zamani a makarantun allo na Jihar Kano aka ruwaito Gwamnan Jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, yana ba da shelar daga wannan rana Gwamnatin Jihar ta haramta barar almajiran makarantun allo a dukkan fadin jihar.

Sanarwar haramcin da bai kamata ta zo wa al’ummar Musulmi, musamman alarammomi da suke da makarantun allon a ba-zata ko wani abin mamaki ba, (kamar yadda zuwa yanzu wadansunsu suke nuna damuwa a kan batun), kasancewar shekaru aru-aru, wadansu mahukunta da al’ummar kasa suke ta yin kiraye-kiraye da fatar lallai a hana wannan tsari na bara na kananan yara,a dukkan jihohin Arewa inda nan al’ada da aka cusa a cikin addinin Musulunci ta samu gindin zama.

Al’adar da ta samu gindin zaman da ya dauko asali shekaru aru-aru, cewa karatun Alkur’ani ba zai samu ga almajiran ba, har sai suna yin bara. Babban abin takaicin shi ne wadansu daga cikin masu ba da wannan fatawa akwai shahararrun malaman addinin Musulunci da a iya cewa tsarin karatun Alkur’anin ya haife su, kuma duk da su sun yi bara, amma ba sa tura ’ya’yansu makarantun allo wani gari balle su yi bara, kuma ’ya’yan nasu suna samun karatun Alkur’ani da na fannonin addinin Musulunci daban-daban da su iyayen ko a mafarki ba su samu ba.

Dadin dadawa irin wadancan manyan malamai sun kewaya kasashen duniyar Musulmi sun ga irin tsarin da kasashen suke bi wajen koya wa kananan yaransu karatun Alkur’ani. Don haka a iya cewa fatawar wadancan manyan malamai ba komai ba ne illa son zuciya da yin amfani da jahilcin mabiyansu don amfanin malaman.

Kamar yadda Gwamna Ganduje ya tabbatar, Gwamnatin Jihar za ta sa ido wajen tabbatar da wannan doka tana aiki a fadin jihar.

An tanadi hukunci mai tsanani a kan mahaifin da aka kama dansa da ke makarantar allo yana yin bara a fadin jihar.

Idan mai karatu bai manta ba a shekarun 1980, wani Gwamnan mulkin soja a Jihar Kano, ya taba yunkurawa wajen hana barace-baracen almajiran makarantun allo da kawo gyara a kan sauran matsalolin rayuwa kamar na yin kayan aure (a lokacin mace-macen aure bai kazanta ba kamar yanzu) da batun  zamantakewa da na ilimin zamani na ’ya’ya mata, ta hanyar kafa kwamitoci da nufin magance su.

Kwamitocin sun yi nasarar kammala ayyukansu tare da mika wa Gwamnan rahotanninsu, rahotannin da Gwamnan ya samu ya fitar da cikakkun bayanan irin yadda gwamnatinsa za ta tunkari matsalolin, amma kwatsam sai aka yi  masa canjin wurin aiki. Abin da ya yi sanadiyyar gwamnonin da suka gaje shi ba su kara waiwayar batun ba, har ga shi yau ana neman shekara arba’in.

Yanzu dai maganar da ake yi, bayan Gwamnatin Jihar Kano ta haramta barar almajiran makarantun allon, jihohin Nasarawa da Neja sun bi sahu.

Jihar Nasarawa har ta dan matsa gaba kadan don ta nuna da gaske take yi a kan haramcin, wajen fara mayar da almajiran makarantun allon da ta tabbatar da ba ’yan asalin jihar ba ne jihohinsu na asali. Jihar Kebbi ma an ce tana kan hanyar hana barace-baracen almajiran makarantun allon yayin da Gwamanatin Jihar Sakkwato ta ce ba za ta hana yin barace-baracen makarantun allo ba, sai ta tattauna da Mai alfarma Sarkin Musulmi da sauran masu ruwa-da-tsaki a kan al’amarin.

Tabbas tunda dai Kano Tumbin Giwa ta fara haramta barar, ko shakka nan da wani dan lokaci za ka ji akasarin jihohin Arewa sun biyo baya.

Batun almajiran makarantun allo da yadda suke yin bara, wata tsohuwar al’ada ce da aka cakuda da addinin Musulunci shekaru aru-aru a tsakanin al’ummar Musulmin jihohin Arewa.

Wadansu iyayen tun asali sun yi imani da fadakarwar (wadansu) malamai na Arewa cewa wanda duk ya tura dansa makarantar allo ko wanda ya aurar da ’yarsa budurwa sadaka, to za su cece shi, har ma ya shiga Aljanna a gobe Kiyama.

Yanzu dai an daina aurar da ’ya’ya mata sadaka, amma tsarin almajirancin makarantun allo da ke tattare da barace-baracen yana ci gaba, har yau.

Ko ba ka yi batun kaskancin da ke tattare da bara ba, to ka kyamaci ta yara kanana masu shekara biyar zuwa abin da ya yi sama da iyayensu suke tura su makarantun allo, ba sutura ko abinci, bare wurin kwana mai kyau, musamman a manyan biranen jihohin Arewa.

Ana zargin  akasarin iyaye ba sa iya daukar nauyin rayuwar yau da kullum na ’ya’yansu, don haka suke tura yaran ba ma don su yi karatu ba, sai don su rika wasu hidimomin neman kudi a biranen suna tura wa iyayen nasu a kauyukansu.

Kwanan baya wannan fili har tsokaci ya yi a kan yadda aka fara kafa makarantar allo ta ’ya’ya mata a Jihar Zamfara. Wannan abu da me ya yi kama muna cikin Karni na 21?

Gaskiyar magana, lokaci ya yi da iyaye za su rika kulawa wajen ba da cikakkiyar tarbiyya da ci da sha da tufatarwa da wurin kwana da ilimantarwa ga kananan ’ya’yansu kuma a gabansu. Lallai iyaye su san cewa Allah ne Ya dora musu wannan hakki. Ga gwamnonin jihohin Arewa, ina ma a ce haduwa suka yi wajen zartar da wannan haramci  baki dayansu, ta yadda ba wani alaramma mai almajiran makarantun allo zai ce bari ya yi kaura daga jihar da aka haramta zuwa jihar da ba a haramta ba.

Ya kuma kamata gwamnonin jihohin Arewa su dai kururuwar almajiran makarantun allo da suke jihohinsu, ba ’yan asalin jihohinsu ba ne har suke mayar da su zuwa jihohinsu na asali. Don kuwa annobar ta barace-barace kowace jiha a Arewa tana da tata, kuma ga mutumin Kudancin kasar nan, shi abin da ya sani shi ne jihohin Arewa kadai ke da almajirai masu bara. Hakazalika haramcin barar ya kamata ya hada har da manya, sannan gwamnonin su bullo da wani tsari na bai-daya da zai kawo dawwamannen gyara cikin harkokin tafiyar da karatun makarantun allo amma ba kowace jiha ta  yi gaban kanta ba. Su ma alarammoni da sauran masu ruwa-da-tsaki su ba da hadin kai.