Search
Subscribe
Makiyaya da manoma kowa ya san hakkinsa

Makiyaya da manoma kowa ya san hakkinsa

Assalamu alaikum Edita. Don Allah ka ba mu dama domin mu isar da sakonmu zuwa ga ’yan uwanmu ’yan Najeriya musamman Fulani makiyaya da kuma manoma cewa, kowa ya san hakkin wani a kansa. Bai kamata a rika kai ruwa rana da juna ba, musamman ku manoma ku nisanci noma a kan hanyar da Fulani suke wucewa wato Burtali don kauce wa ganin laifinsu. Noma hanyar da suke bi suna wucewa sun dawo suna bi a bakin titi wanda hakan yana sanya a buge musu dabbobinsu yayin da suke wucewa zuwa wajen kiwon dabbobinsu. Mu sani su ma ’yan kasa ne suna da hakkin su je ko’ina a cikin fadin kasar nan. Daga karshe muna kira ga Fulani makiyaya su guji yi wa manoma barna a domin samun zaman lafiya a kasarmu Najeriya. Mun gode Edita Allah Ya taimaki wannan kamfanin da yake ba mu damar aika sakonmu ga wuraren da ba mu iya kaiwa amin.

Daga Nasiru Musa Maiyama Jihar Kebbi 08062206733 da Alhaji Bilya Doya Zauro Jihar Kebbi 07067467444.

Kira ga Gwamnan Zamfara

Edita, ina son ka ba ni dama in yi kira ga sabon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawallen Maradu cewa ya ji tsoron Allah ya share wa talakawan Jihar Zamfara hawaye, Allah Ya ba shi sa’a.

Daga Sanusi Musa Police, Gusau, JIhar Zamfara 08139005478.

Jinjina ga jami’an tsaro kan ceto Magajin Garin Daura

Salam Edita, don Allah ka ba ni dama in yi jinjina da yabo ga jami’an tsaronmu. Hakika kubutar da Magajin Garin Daura da jami’an tsoro suka yi abin a yaba ne. Allah Ya kawo mana karshen wannan lamari na yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, amin summa amin.

Daga Sani Mohammad Chindo, Unguwar Karofin Madaki, Bauchi, 08030918913.

 

Ganduje na mika godiyarsa

ga matan Kano

Assalamu alaikum, ’yan uwana mata. Ina fata kuna lafiya ina mai shaida muku cewa Gwamnatin Kano ta Ganduje tana kara mika godiyarta zuwa gare ku kan jajircewar da kuka yi wajen ganin ya sake jan ragamar mulkin Jihar Kanon Dabo. Kuma yana nan yana shirin sake bullo muku da wani tallafi domin dogaro da kawunanku, mun gode.

Daga Balkisu Sani Dala, Shugabar Mata ta  APC  Kano ta Tsakiya. 08162136693.

 

Kira ga Gwamnan Bauchi

Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad, kan ya yi wa Allah ya dubi al’ummar da suke Unguwar Karofin Madaki da idon tausayi ya gyara musu hanyarsu da ta tashi daga Kofar Fadar Sarkin Bauchi zuwa Railway. Hakika hanyar tana bukatar gyara ganin yadda gwamnatocin da suka shude suka yi biris da ita bisa la’akari da wannan hanya tana daga cikin manyan hanyoyi a cikin garin Bauchi. Daga karshe nake addu’an Allah Ya sa wannan kira nawa ya kai ga inda ya dace.

Daga Sani Mohammad Chindo, Unguwar Karofin Madaki, Bauchi, 08030918913.

 

Kubutar da Magajin Garin Daura

Assalamu alaikum Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi yabo da jinjina ga jami’an tsaron da suka kubutar da Magajin Garin Daura. Da fatar Allah Ya kara bai wa jami’an tsaron Najeriya nasarar dakile garkuwa da mutane, amin.

Daga Garba Sabiyola Sa’idawa, Gashuwa 07061636664.

 

A inganta makarantun Yobe ya fi kai daliban jihar waje

Salam Edita. Hakika mu al’ummar Jihar Yobe mun gamsu da matakin da Gwamnan Jihar Alhaji Mai Mala Buni yake dauka a bangaren ilimi a jihar, to amma wani hanzari ba gudu ba, batun shirin fitar da daliban jihar zuwa kasashen ketare da gwamnatin take kokarin yi, shi ne muke da kokwanto a kansa, lura da cewa irin wannan tallafi yana karewa ne kawai a tsakanin ’ya’yan manya masu uwa a gindin murhu. Saboda haka muna kira ga Gwamna Buni ya soke wannan kudiri na fitar da yaranmu zuwa kasar waje, maimakon haka zai fi kyau a inganta makaratun jihar da kayan aiki na zamani, sannan a kara wa malamai albashi.

Daga Idriss M. Idriss, Damaturu, Jihar Yobe, 08033775767.

 

Jan hankali ga matasa

Assalam Edita. Ina jan hankalin matasa  cewa, kamata ya yi mu daina bin rudu wajen zaben jagora, mu rika tsayawa muna duba wane shugaba ne yake kaunarmu wanda zai kawo mana abubuwan da za su inganta rayuwarmu. Kamar samar mana da ilimi, sana o’i, aikin yi da kuma hana mu shaye-shaye kamar yadda wani tsohon Gwamna ya yi ta daukar ’ya’yan talakawa yana fitar da su zuwa kasashen ketare neman ilimi. Allah Ya saka masa da alheri, amin.

Daga Rabi’u Ibrahim CKK, 08135421198.

 

Kira ga Shugaba Buhari

Shugaban Kasa ka dube mu da idon basira ana neman a hana mu abin da za mu sa a bakin salati a gonakinmu. Ana bin mu ana kashewa, to yanzu so ake yi mu zauna gida, mu ci me? ya kamata a dubi wannan lamari.

Usman 440, Malumfashi, 08135815119.

 

Kira ga Gwamnan Jihar Kaduna

Don Allah Edita, ka isar min da kirana ga Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i da ya bi shawarar malaman addini ya watsar da dokar rajistar binne gawa. Ya Mai girma Gwamna ka sani mutanen Jihar Kaduna kashi 75 cikin 100 Musulmi ne kuma wannan dokar a kansu za ta fada, kuma ta saba wa karantarwar addinin. Mutum zai ji da abin da zai ci ne ko da biyan Naira 5000? Muna rokon Mai girma Gwamna ya kalli karantarwar addini ya yi watsi da wannan dokar.

Daga Abubakar Ibrahim Umar Zariya 08060884760.

 

Kira ga Shugaban Najeriya

Assalam Edita. Shugaban Najeriya Buhari, ka sallami ’yan fadarka masu ba kasarmu ciwon kai ka zabo masu kishi irinka. Baba a mulkinka karo na biyu kada ka sassauta wa duk wanda aka kama da laifi.

Daga Sufiyanu Aliyu Addan Yabo SKK, 09057924575.

 

Gaisuwa ga gwamnonin Zamfara da Sakkwato

Assalamu alaikum ma’aikatan jaridar Aminiya, ingantacciyar jarida mai albarka. Don Allah ina son ku mika min sakon gaisuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawallen Maradun da amininsa Matawallen Sakkwato, Allah Ya ba jiharmu Zamfara zama lafiya da Najeriya baki daya.

Daga 07030705096.

 

Zaben Zamfara: Mun amince

da hukuncin kotu

Salam, Aminiya ku fada wa duniya, cewa mun yi na’am da hukuncin kotu, kan dambarwar zaben Jihar Zamfara, tare da fatar sauyin gwamnatin da aka samu daga APC zuwa PDP, ya zamo silar fitar Zamfarawa daga halin taskun da suke ciki, amin.

Daga Dahiru Dauda (KGY) Bindawa, 08055552897.

 

Karshen alewa kasa

Assalam Aminya. Ina so in yi amfani da wannan damar wajen taya Mai girma Gwamnan Bauchi murna da fatan zai bai wa marada kunya.

Daga Nuraddin I. Ningi, 08038488775.

 

Taya murna ga gwamnoninmu

Salam Edita. Ina so ka isar min da sakon taya murna ga zababbun gwamnonin jam’iyyarmu ta PDP. Da fatar Allah Ya taya su riko da adalci ga talakawan da suka dora musu amana amin. Bayan haka ina yi wa al’ummar Zamfara jaje da bala’in da yake faruwa a jihar  da kuma murnar samun nasara.

Daga 08140881207.

 

Addu’a ga Shugaban Najeriya

Assalamu alaikum. Shugaba Buhari Allah Ya ba ka ikon cika alkawarin da ka yi wa ’yan Najeriya, kuma Ya kara maka lafiya, amin.

Daga Isah Murtala Gamagira. 08135419744.

 

Fatan alheri ga sababbin

masu mukamai

Ina yi wa sababbin masu mukamai da tsofaffi murna. Da fatan Allah Ya taya ku riko.Ku waiwaya baya sannan ku yi tunani da bayin Allah da suka zabe ku, talakawa ke nan. Akwai hisabi ranar gobe.

Daga Isah Murtala Gamagira, 08135419744.

 

Kira ga jam’iyyar APC

Salam Edita. Ka ba ni dama isar da sakona ga Jam’iyyar APC daga Buhari sai Kwankwaso ko El-Rufa’i ko kuma mu bar ta gaba daya mu koma PDP.

Daga Angon Raheenat K.M Kano 08063844790.

 

Aminiya ce aminiyata

Assalamu alaikum bayan gaisuwa da jinjina da fatan alheri. Gaskiya ni dai na zabi AMINIYA a matsayin aminiyata yadda kuke tsage gaskiya komai dacinta musamman, Ado Sale Kankiya, sai dai mu ce Allah Ya saka muku da alheri Ya tsare mana ku a duk inda kuke amin.

Daga Dan’asabe Mai Zazzau Filin Black Star Unguwar Daji, Minna Jihar Neja, 09069405541.

 

Kisan gilla a Arewa: Kira

ga Shugaba Buhari

Don Allah ku ba ni dama in yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ake kashe bayin Allah a yankinsa na Arewa, ya tuna dukkan wata rai da ta salwanta Allah zai tambaye shi. Allah Ya kawo mana agaji.

Daga Dahiru Yahaya, Jihar Bauchi, 08175745774.

Bindiga

Assalam Edita, don Allah ka bani dama in kai kukana ga shugaban kasar mu Baba Buhari, don Allah a bude boda kuma duk wanda bincike yasa aka gano shi akan daukar nauyin ’yan bindigar da suka addabi Zamfara da yankinmu a kashe shi nan ta ke.

Daga Abdulrahaman Garba Toka Funtuwa 08038293121.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin