✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makusantan Jonathan sun fice daga PDP zuwa APC

Wadansu makusantan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan sun fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Wadanda suka canja shekar sun hada da Cif Enogha Robert da…

Wadansu makusantan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan sun fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Wadanda suka canja shekar sun hada da Cif Enogha Robert da Cif Claudius Enegesi. Mutanen sun sauya sheka ce zuwa APC a wajen kaddamar da yakin neman zabe da dan takarar Gwamna na APC ya fara a Karamar Hukumar Ogbia, don tunkarar zaben Gwamnan Jihar dake tafe a ranar 16 ga Nuwamba.

Cif Enogha ya taba rike mukamin Kwamishinan Muhalli na Jihar Bayelsa. Kuma yana daya daga cikin manyan masu fada-a-ji a Karamar Hukumar Ogbia. Enegesi kuwa na hannun damar tsohon Shugaban Kasa Jonathan ne na sosai, wanda ya taba rike mukamin Shugaban Majalisar tsohuwar Jihar Ribas, kuma shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP na farko a Bayelsa, kuma daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar a Karamar Hukumar Ogbia.

Hakazalika a  Karamar Hukumar Nembe ma Jam’iyyar APC ta yi babban kamu inda Cif Bright Erewari-Igbeta ya sauya sheka zuwa APC.

Bright tsohon dan Majalisar Bayelsa ne kuma shi mai bai wa Gwamnan Jihar Shawara kan kula da  Muhalli, kafin ya ajiye mukaminsa ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Har ila yau, akwai Cif James Jephathah wanda aka sani da Octopus, shi ma ya ce babu shi ba PDP. Ya koma APC kuma ya yi alkawarin cewa shi da magoya bayansa sai sun raba Jihar Bayelsa da mulkin PDP.