✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mala Buni zai kawo ci gaban da ake bukata a Yobe – Kingibe

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ambasada Babagana Kingibe, ya ce yana da yakinin Gwamna Mai Mala Buni zai kai Jihar Yobe matakin ci gaba.  Jakada Babagana…

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ambasada Babagana Kingibe, ya ce yana da yakinin Gwamna Mai Mala Buni zai kai Jihar Yobe matakin ci gaba.  Jakada Babagana Kingibe ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar taya murna ga Gwamnan a garin Damaturu, ya ce a matsayinsa na gogaggen dan siyasa, kuma tsohon Sakataren Jam’iyyar APC ta Kasa, wanda yake da fada da cikawa ba ya shakka Gwamna Buni zai bai wa kowa mamaki a jihar.

Ya ce “Ina farin cikin yadda al’ummar Jihar Yobe suka kirawo ka domin ka zo ka bad a gudunmawarka wajen ci gaban jihar, kuma za ka iya don na san matsayinka kuma ina da yakinin cewa al’ummar Jihar Yobe sun yi zabin da ya dace. Kuma ba na shakka za ka bai wa marada kunya a kowane lokaci.”

Ya kara da cewar a matsayinsa na wanda ya san siyasar Jihar Yobe, kuma ya rike Sakatariyar Jam’iyyar APC  a kasa, babu wani abu da zai hana shi gudanar da kyakyawan shuganbanci kuma ya kai jihar zuwa wani babban matsayi. Tsohon Jakadan ya yi magana a kan amincewar da Shugaba Buhari yake da ita a kan Gwamna Mai Mala Buni, ya ce Shugaban a koyaushe yakan yi magana a kan irin kyawawan halayensa. Sai Jakada Kingibe ya bai wa Gwamnan tabbacin a shirye yake domin ba da shawarwari don samun nasarar gwamnatinsa.

Da yake jawabi, Gwamna Mai Mala Buni ya gode wa Ambasada Kingibe  kan wannan ziyara da ya kawo, kuma ya ce al’ummomin jihohin Yobe da Borno suna alfahari da irin gudunmawar da Ambasada Kingibe yake bayarwa wajen ci gaban dimokaradiyya a kasar nan.