Search
Subscribe
Malaman Jami’a 2 da aka yi garkuwa da su sun kubutar da kansu

Dakta Adamu Chonoko da Dakta Umaru Chonoko

Malaman Jami’a 2 da aka yi garkuwa da su sun kubutar da kansu

Malaman Jami’an nan biyu yan uwan juna watau Dakta Adamu Chonoko ‎na jami’an Ahmadu Bello Zariya da kuma Dakta Umaru Chonoko na Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Kaduna sun yi nasarar gudowa daga hannun masu garkuwa da su a yau Lahadi.

A cewarsu, sun yi tafiyar sa’a 13 a cikin daji kafin suka iso cikin garin Kaduna da misalin karfe 11:51 na safiyar Lahadi.

Dakta Adamu Chonoko, wanda shi aka fara kamawa a gidansa da ke a unguwar Mahuta Kaduna ya bayyana cewa bai taba ganin tashin hankali ba sai a wannan rana.

Shima dan uwansa Dakta Umar Chonoko, wanda shima aka kama bayan ya kai wa masu garkuwa da mutanen kudin fansar, dan uwan nasa amma sai suka rike shi tare da neman karin kudi.

Sun bayyanawa Aminiya cewa, “Allah ne Ya sa masu gadin mu suka yi barci daga nan muka silale muka shige cikin daji. Tun karfe 11:30 na dare muke tafiya har karfe 11:51 na wayarwar garin Lahadi,” in ji shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin