✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malaman jami’o’i na dada kawo koma-baya – Kwamared Aminu Tilde

Wani dan gwagwarmayar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma, kuma Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa na shiyyar Arewa ta Tsakiya (JTNTY), Kwamared Aminu Sale Tilde…

Wani dan gwagwarmayar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma, kuma Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa na shiyyar Arewa ta Tsakiya (JTNTY), Kwamared Aminu Sale Tilde ya ce malaman jami’o’in Najeriya suna daya daga cikin masu mayar da kasar nan baya.

Kwamared Aminu Sale Tilde ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, inda ya ce a duk lokacin da suka tashi yin fada da gwamnati ba su da wani abin yi sai yajin  aiki, wanda yin hakan ba ya cutar da gwamnatin da komai, sai dai ya cutar da al’ummar Najeriya tare da kawo koma-baya.

A cewarsa, malaman jami’o’in nan gwamnati tana biyansu kudaden bincike da karantar da daliban da suke yi da kuma daukar nauyin biyan kudaden karatun da suke yi, idan an dauke su aiki, har su zama farfesoshi.

Ya ce da malaman jami’o’in suna yajin aikin yadda ya kamata da yajin aiki ba zai zamanto musu hanya da za su rika yin fada da gwamnati ba, domin idan sun yi yajin aikin gwamnati ba ta jin komai, sai dai ’ya’yan talakawa ne suke shan wahala.

Ya ce a kullum malaman jami’o’in  Najeriya suna nuna wa mutane cewa sun fi kowa gaskiya da adalci a Najeriya, wanda hakan ba gaskiya ba ne.

Sannan ya ce a doka malamin jami’a bai kamata ya rika koyarwa a jami’a fiye da guda ba. Amma a Najeriya akwai malaman jami’a da suke koyarwa a jami’o’i fiye da biyar.

Ya yi  kira ga gwamnati  ta tabbatar ta shigar da malaman jami’o’i a tsarin biyan albashi na bai-daya. Kuma ta nada wani kwamiti da zai rika bin abubuwan da suke faruwa a jami’o’in Najeriya.