✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malaman S. Power na Sakandare zasu shiga yajin aiki a Katsina

Kungiyar malaman sakandire a karqashin shirin S. Power wanda gwamnatin Masari ta bullo da shi domin inganta ilmi a Jahar na kokarin shiga wani yajin…

Kungiyar malaman sakandire a karqashin shirin S. Power wanda gwamnatin Masari ta bullo da shi domin inganta ilmi a Jahar na kokarin shiga wani yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 7 ga watan Oktoba 2019 da muke ciki akan rashin biyan su albashi har na tsawon watanni 5. Shugaban Kungiyar na Jiha Kwamared Aliyu Dahiru Kaita ya shaidawa wakilin Aminiya hakan a yau Alhamis.

Ƴan Kungiyar sun ce sun zabi matakin tafiya yajin aikin ne saboda rashin samun wani cikakken bayani akan biyansu albashin har na wata 5. “Mun bi duk wata hanya domin ganin cewa mun samu wannan haqqi namu kamar yadda muke jin labarin cewa, Gwamna Masari na bayar da ummarnin biyan namu amma har yanzu shiru.

Cikin wadannan kudade na wata 5, muna bin kudin wata 3 a ofishin Darakta akan harkokin siyasa wanda shi ne sakataren wannan shiri a karkashin ofishin Sakataren Jaha, kafin mayar da albashin namu a ma’aikatar ilmi ta Jaha wadda su kuma a yanzu muke bin wata 2.

Yana da kyau kamar yadda muka tsare aikinmu bisa ga yarjejeniyar da aka yi, to ba sai an bari munci bashin da zai zamo mun kasa biya ba balle a bamu wasu. Wasu an tura wasu Kananan hukumomin da basu da wajen zama a can, dole suyi amfani da abin hawa kafin su je, sannan ga batun abinci. Amma ace har anyi watanni 5 babu ko sisi kuma babu wani cikakken bayani akai? Yana da kyau Gwamna da gwamnatinsa da duk wani mai ruwa da tsaki akan wannan da su duba don daukar matakin gaugawa kafin wancan wa’adin da mu kanmu bada son ran mu muka dauke shi ba, don warware matsalar.