✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malami ya gina Gidan Marayu a Jos

Wani fitattacen malamin addinin Musulunci kuma Daraktan Gidauniyar Anwarul Faidah, Sheikh Harisu Salihu ya gina wani babban gidan marayu a Jos fadar Jihar Filato. Da…

Wani fitattacen malamin addinin Musulunci kuma Daraktan Gidauniyar Anwarul Faidah, Sheikh Harisu Salihu ya gina wani babban gidan marayu a Jos fadar Jihar Filato.

Da yake jawabi a wajen bude gidan marayun, Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato, Malam Muhammad Ahmed Nazifi ya bayyana cewa gina gidan marayu yana daya daga cikin ayyukan  sadaka mai gudana (Sadakkatul  Jariya.)

Kwamishinan ya ce gidan marayun shi ne irinsa na farko da wani mutum daya ya gina kuma shi ne na farko a cikin al’ummar Musulmin Jihar Filato. Domin dukan gidajen marayun da ake da su a jihar, kungiyoyi ne suka gina. Sai ya yi kira ga sauran al’umma su yi koyi da wannan mutum wajen gina irin wadannan gidaje, domin tallafa wa marayu.

A jawabin Sakataren Gudanarwar Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Jihar Filato, Sheikh Abdul’azeez Yusuf ya yi kira ga kungiyoyin addinin Musulunci da sauran kungiyoyi masu zaman kansu su bai wa wannan gidan marayu goyan baya da hadin kai.

Ya ce babu shakka wannan gidan marayu wuri ne da ya kamata a taimaka masa.

Shi ma a nasa jawabin wani Babban Darakta a Ma’aikatar Mata ta Jihar Filato, Mista Joseph Gwaisan ya yi bayanin cewa sun bai wa wannan gidan marayu izinin gina gidan ne ba tare da bata lokaci ba, domin an cika dukan ka’idojin da suka kamata.

Tun farko a jawabin wanda ya gina gidan marayun Sheikh Harisu Salihu ya bayyana cewa babban abin da ya karfafa masa gwiwar gina wannan gida, shi ne ganin irin mawuyacin halin da marayu suke ciki. Don haka ya gina  gidan domin ya tallafa wa marayun.

Ya ce wannan aiki da ya yi bai dauka ya yi wani abu ba. Kuma tunda ya fara aikin babu wani dan siyasa da ya taimaka masa.

Ya ce wannan gida zai dauki marayu  40 ne, maza  20 da mata  20. Ya ce suna da ma’aikata 14  da za su rika aiki a gidan ana biyansu albashi duk wata.

“Wadannan marayu guda 40, mun dauki ’yan shekara 5 ne za mu rike su har su kai shekara 13 kafin mu yaye su. Za a rika yi musu abinci a kullum. Kuma za mu sanya su a makarantarmu muna son kafin mu yaye su, su haddace Alkur’ani Mai girma”.