✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamin makaranta ya yi wa ’yar shekara 7 fyade

Ana zargin wani malami mai suna Danlami Abubakar da ke koyarwa a Makarantar Firamare ta Narayi a Kaduna da yi wa daliba ’yar shekara 7…

Ana zargin wani malami mai suna Danlami Abubakar da ke koyarwa a Makarantar Firamare ta Narayi a Kaduna da yi wa daliba ’yar shekara 7 fyade, a ranar 20 ga Mayun da ya gabata.

Aminiya ta gano cewa wanda ake zargin yana koyar da ilimin kwamfuta ne a makarantar. Danlami, ya yi amfani da wani ginin da ba a karasa ba kusa da makarantar lokacin da dalibar ta je yi fitsari.  Mahaifin yarinyar ya shaida wa Aminiya  ’yarsa ta dawo daga makaranta rike da Naira 100. “Ta ta dawo daga makaranta rike da Naira 100 a lokacin ba na gida mahaifiyarta ma ta je unguwa amma a ranar ta dawo. Wani makwabcinmu ne ya sanar da mahaifiyarta cewa ya ga kudi a hannunta.

“An tabbatar an yi wa yarinyar fyade a Asibitin Yusuf Dantsoho, daga nan aka ce mu dawo washegari mu  karbi sakamakon gwajin. A lokacin da na je karbar gwajin sai aka shaida min cewa wata ’yar sanda ta zo ta karba,” inji shi.

Ya ce tun daga lokacin aka hana shi sakamakon gwajin ’yarsa, abin da kadai aka ba su shi ne maganin da aka rubuta a asibitin. Ya ce kwanaki kadan sai ’yarsa ta kamu da matsanancin ciwon mara. “Nan da nan na kira mahaifin wanda ya yi fyaden na fada masa abin da ke faruwa, kamar yadda ya ce mu kira shi duk lokacin da ’yarmu ta koka a kan wani ciwo. Na kira shi amma ya ki amsa kirana. Sai na tafi neman bashi domin zuwa asibiti,” inji shi.

A lokacin da aka tun tubi Rundunar ’Yan sandan Kaduna, Kakakinta Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin yana gaban kotu.  Ya ce “An dauke korafin daga ofishin ’yan sanda na Narayi zuwa na Binciken Manyan Laifuffuka (CID) don bincike. Kuma sun kammala binciken sun mika batun ga kotu.”