Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mambobin PDP 5 sun rasu a hadarin mota a Sakkwato

Rahotanni na bayyana cewa, mambobin jam’iyyar adawa ta PDP biyar sun rasu sanadiyyar hadarin mota da ya faru a titin Sakkwato zuwa karamar hukumar Isa ranar Litinin.

Kimanin mambobin jam’iyyar 14 ne suka samu munanan raunuka a hadarin yayin da wasu mutum 49 suka jikkata.

ADVERTISEMENT

Mambobin sun  yi hadarin ne yayin da suke koma wa unguwar Bargaja da ke Karamar hukumar Isa jihar Sakkwato bayan halartar kaddamar da kamfen din dan takarar shugaban Najeriya na PDP da aka yi a dandalin Kangiwa square a Sakkwato.

ADVERTISEMENT