✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester City ta samu kyautar Naira Biliyan 18

  Kulob din Manchester City da ke Ingila ya samu zunzurutun Fam Miliyan 38 da dubu 400 kimanin Naira Biliyan 18 da miliyan 864 saboda…

 

Kulob din Manchester City da ke Ingila ya samu zunzurutun Fam Miliyan 38 da dubu 400 kimanin Naira Biliyan 18 da miliyan 864 saboda nasarar lashe gasar firimiyar Ingila a bana.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da kulob din yake lashe wannan kofi.

An kammala gasar ta bana ce a ranar Lahadin da ta wuce inda kulob din ya zo na daya bayan ya lallasa na Brighton da ci 4-1.

Kulob din Liberpool ne ya zo na biyu, inda ya samu kyautar Fam Miliyan 36 da dubu 500 kimanin Naira Biliyan 17 da miliyan 171 yayin da kulob din Chelsea wanda ya zo na uku a gasar ya samu kyautar Fam Miliyan 34 da dubu 600 kimanin Naira Biliyan 16 da miliyan 269.

Kulob din Manchester United ne ya fi yawan lashe wannan gasa a tarihi amma a bana kulob din ya kare ne a matsayi na 6.