✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mandzukic zai koma Manchester United

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Jubentus na Italiya sun ce dan kwallonsu  Mario Mandzukic ya kammala shirin komawa kulob din Manchester United da…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Jubentus na Italiya sun ce dan kwallonsu  Mario Mandzukic ya kammala shirin komawa kulob din Manchester United da ke Ingila da zarar an bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a watan Janairu mai zuwa.

Wata jaridar labaran wasanni TuttoSport ta Italiya ce ta kalato wannan labari, inda ta ce tuni kungiyoyin biyu suka shiga tattaunawa game da yiwuwar canja shekar dan kwallon.

Mandzukic wanda ya koma Jubentus daga kulob din Atletico Madrid na Spain a 2015 bai yi wa Jubentus wasa ko daya a kakar bana ba. Saboda zaman da yake yi a benci ne ya sa ya yanke shawarar canja sheka zuwa United.

Da farko ya nemi komawa wani kulob ne a kasar Katar amma da cinikin bai kaya ba sai ya yanke shawarar komawa United da ke Ingila.

Ana sa ran United za ta saye shi ne a kan Fam miliyan 9 (kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 157).  Sannan za ta rika biyansa albashin Fam miliyan 4 da dubu 400 (kimanin Naira biliyan 2 da miliyan  172) duk shekara.  Ana sa ran zai kulla yarjejeniyar shekara 1 da rabi ne da United.

Mandzuki dan asalin kassar Kuroshiya, yanzu haka yana da shekara 33.  Ya yi wa Jubentus wasa sau 162 inda ya zura kwallo 44 a raga.