Manjo Hamza Almustafa, wanda ya yi kwanaki 39 da fitowa daga gidan kurkuku, bayan ya kwashe shekaru 15 a tsare bisa zarginsa da aikata laifuffuka 4, ciki har da kashe matar marigayi Cif Abiola, aka yanke masa hukuncin kisa a ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2011, ya yi tsokaci kan daukaka karar da Jihar Legas ta yi.
Bayan yanke wannan hukunci ne, sai ya daukaka kara, inda wasu alkalai 3 karkashin Mai shari’a Amina Augie suka yi watsi da karar. Bayan hukuncin ne sai gwamnatin Jihar Legas ta daukaka kara tare da hujjoji 14 da ta ke jin bai dace a ce an sallami mutanen biyu ba.
Yayin da wakilin Aminiya ya tuntubi Manjo Almustafa kan haka, sai ya ce ko jikinsa, domin tun farko karya ce ta daure su kuma gaskiya ta sake su don haka ko sau nawa gwamnatin za ta daukaka kara wannan ba abin damuwa ba ne a gare shi.
Ya ce gwamnatin jihar ta Legas, tana da ’yancin daukaka kara domin ba wani abu ne ta yi sabo ko kuma wanda ya saba wa dokar kasa ba, lamarin da shi ma tuni ya sanar da lauyoyinsa domin sanin matakin da za su dauka game da wannan yunkurin.
Manjo Almustafa ya ce wannan ba zai rage shida kome ba domin kuwa a halin yanzu shi mutum ne mai cikakken ’yanci kuma zai ci gaba da walwala kuma wannan daukaka karar zai kara tono wasu abubuwan da a da ’yan Najeriya ba su san da su ba. Ya yi kira ga masoyansa da kar wannan lamari ya razana su.
Manjo Hamza Almustafa: Ba na shakkar daukaka karar da Jihar Legas ta yi
Manjo Hamza Almustafa, wanda ya yi kwanaki 39 da fitowa daga gidan kurkuku, bayan ya kwashe shekaru 15 a tsare bisa zarginsa da aikata laifuffuka…