✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma 2000 daga Jihar Borno sun kaura zuwa Yobe

Kungiyar Manoma ta Yankin Arewa maso Gabas (NECAS), ta ce manoma 2000 ’yan asalin Jihar Borno ne suka yi kaura zuwa Jihar Yobe da zimmar…

Kungiyar Manoma ta Yankin Arewa maso Gabas (NECAS), ta ce manoma 2000 ’yan asalin Jihar Borno ne suka yi kaura zuwa Jihar Yobe da zimmar samun ingantaccen amfanin gona a yankin Arewa maso Gabas.

Shugaban NECAS na Kasa, Alhaji Sadik Umar Jaware ne ya bayyana haka yayin kaddamar da raba taraktocin noma 100 ga manoma a kananan hukumomin jihar, 17.

Shugaban NECAS din, wanda Sakataren Kungiyar Alhaji Ahmed Muhammed Dukku ya wakilta, ya ce wannan karamci, an yi shi ne da niyyar bai wa manoman da aka raba da muhallansu, damar noma a gonakin Jihar Yobe, don samun dogaro da kai, tare da wadatar cimaka a yankin.

Sai dai ya nuna rashin jin dadinsa, game da abin da ya kira, barin yankin a baya da a ka yi, ta fuskar damawa da shi a tsare-tsaren noma na gwamnati-wanda hakan ne ya zaburar da su, wajen kafa kungiyar da nufin habaka noman zamani a yankin.

“Za mu rabar da taraktocin noma 600, a daukacin yankin. Sai dai, bisa la’akari da bukatar da Jihar Yoben ke da shi ga NECAS, muna kaddamar da raba taraktocin 100, a jihar, domin inganta noman zamani,” inji shugaban.

Da yake kaddamar da raba taraktocin, Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, ya shawarci manoman su rungumi noman zamanin da nufin tada komadar tattalin arzikin jihar, wanda ta’addacin Boko Haram ya gurgunta.

A cewar Gwamnan, babu kasar da za ta bugi kirjin cewa karanta ya kai tsaiko, har sai tana iya ciyar da al’ummarta. Sa’annan ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Jihar a shirye take ta kulla kawance da dukkan kungiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu, wajen bunkasa noma a jihar.