Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Manoma dubu 10 za su amfana da tallafin Bankin Duniya

Tarakta tana aikin huxa a wata gona

Akalla manoma dubu 10 da ke Jihar Kogi ne za su amfana da tallafin Dalar Amurka miliyan 200, (kimanin Naira biliyan 71 da miliyan 964 da dubu 1 da 592) da Bankin Duniya ya sanar domin bunkasawa tare da adana kayan da aka noma a shirin tallafa wa manoma, na APPEALS   .

Shirin dai zai kasance na tsawon shekara bakwai, inda zai fi mayar da hankali ne a kan  tallafa wa mata da matasa domin habaka bangaren samar da kayan  gona da kuma sarrafa su wadanda suka hada da  shinkafa da yazawa da kuma rogo.

ADVERTISEMENT

Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa-da-tsaki Jami’in Kula da Shirin a Jihar Kogi, Dokta Sani Abdullahi Ozomata, ya ce Jihar Kogi da takwarorinta; Kano da Kaduna da Enugu da Kuros Ribas da kuma Legas suna daga cikin wadanda aka zaba domin gudanar da shirin.

Jami’in ya kara da cewa, aiwatar da shirin APPEALS a jihar zai fi mayar da hankali ne a kan nau’o’in uku na kayan gona .

ADVERTISEMENT

Dokta Sani, ya ce makasudin shirin shi ne samarwa da kuma sarrafa kayan gona domin tabbatar da cewa manoma sun bunkasa nomansu zuwa tsarin ci gaba na kanana da matsakaitan masana’antun noma.

Ya ce, “Za mu bayar da tallafi ga manoma na asali ba ’yan siyasa masu fakewa da noma ba, haka zalika shirin zai duba bangaren samar da hanyoyi da sauran kayyayakin da za su bunkasa aikin domin sadar da monama da gonakinsu cikin sauki.”