✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma dubu 11 ne za su amfana a shirin Appeals na shekara 5

Shugaban shirin bunkasa aikin gona da sarrafa shi tare da bunkasa rayuwar al’umma na kasa (APPEALS), na Jihar Kaduna, Dokta Yahaya Aminu ya tabbatar wa…

Shugaban shirin bunkasa aikin gona da sarrafa shi tare da bunkasa rayuwar al’umma na kasa (APPEALS), na Jihar Kaduna, Dokta Yahaya Aminu ya tabbatar wa manoma cewa sana’ar noma tana taimaka wa rayuwa da zamantakewar al’umma.

Ya bayyana haka ne a wajen taron masu ruwa-da- tsaki da shirin ya gudanar don fadakar da manoma da masu kananan masana’antu alfanun da shirin APPEALS ke da shi a taron da ya gudana a dakin taro na Kongo da ke Zariya.

Dokta Yahaya Aminu, ya yi nuni da cewa harkar noma na kawar da kwadayi da dibar kayan da ba naka ba musamman kayan gwamnati.

A cewar shugaban shirin, harkar noma tana samar da hanyoyi masu yawa da manomi zai samu kudaden shiga ta yadda zai dogara da kansa.

Ya ci gaba da cewa wannan shirin ana yin sa ne kan masara da citta da kuma samar da madara ta hanyar kiwon shanu.

Dokta Aminu ya bayyana cewa manoma dubu 11 ne za su amfana a wannan shirin na shekara biyar kamar yadda tsarin yake .

Taron ya samu halartar kungiyoyi da masu kananan masana’antu da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar noma da ke fadin Jihar Kaduna.