✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma masu bukata ta musamman za su fara samun tallafin noma a Kano

Shirin Ingantawa da Fadada  Harkar  Noma da kuma tallafa wa rayuwa (APPELS) ya bayyana cewa sama da manoma dubu daya ne daga cikin nakasassu za…

Shirin Ingantawa da Fadada  Harkar  Noma da kuma tallafa wa rayuwa (APPELS) ya bayyana cewa sama da manoma dubu daya ne daga cikin nakasassu za su amfana da shirin tallafin noma da kungiyar za ta fara yi a Jihar Kano.

Ko’odinetan shirin na APPPELS Malam Hassan Ibrahim ne ya bayyana haka a taron wayar da kai na yini daya da aka shirya wa masu bukata ta musamman a Kano.

A cewar Ko’odinetan shirin ya samu tallafi ne daga Bankin Duniya da gwamnatocin tarayya da ta Jihar Kano. An kuma kirkiro shi ne da manufar inganta harkar sarrafawa da karin daraja da yadda za a samar wa mata da matasa ayyukan yi da nufin shawo kan irin asarar da ake yi bayan an gama girbi da sauran matsalolin da ke ci wa kananan manoma tuwo a kwarya dangane da abin da ya shafi noman shinkafa da tumatir da alkama.

Malam Hassan ya bayyana cewa an shirya taron ne da nufin sanar da nakasassu  damar da shirin da yake nufin ba su don su shiga a dama da su a cikin harkar noma gadan-gadan.

Ya kara da cewa shirin ya tsara cewa daga cikin wadanda za su amfana da shirin na kimanin manoma dubu 10, dole kashi 10 cikin 100 su zamo nakasassu ne.

Lokacin da yake yi wa mahalarta taron jawabi kwararre a kan abin da ya shafi ci gaban rayuwar mata da matasa na shirin, Malam Usman Muhammad ya bayyana cewa shirin zai tallafa ne kadai a bangarorin da manoman suka zaba da kansu.

Ya kara da cewa za a ba nakasassu horo na musamman don su san abin da ake nema daga gare su kafin su cika sharuddan samun tallafin shirin.